Talauci lamari ne da miliyoyin al’umma ke fuskanta a sassan duniya. Wannan ne babbar dalilin da mutane fiye da 100,000 suka yi gangami a garin Paris ta kasar Faransa a ranar 17 ga watan Oktoba na shekarar 1987 don tattaunawa tare da dubi ga mutanen da ke fama da tsananin talauci a duniya.
Rana ce da aka ware don fadakar da al’umma duniya a kan bukatar samar da hanyoyin kawo kaeshen talauci ta duk hanyar data fito. Rana ce da ake nazari don samar da hanyoyin fitar da dimbin al’ummar da ke fuskantar talauci da dukkan abubuwan da sukan taso sakamakon taualci a cikin al’umma wadanda suka hada da tashe-tashen hankali, cututtuka da rashin muhalli.
Al’umma duniyna amfani da lokacin don karfafa tattauawa da fahimtar juna a tsakanin mutane da rayuwa ke a cikin talauci da kuma al’umma duniya gaba daya.
Ta nan ne ake samun yanayin tattaunawa da sauraron matane masu fama da talauci don fahimtar cikakken halin da suke ciki tare da tattauna yadda za a tallafa musu.
Amma a daidai wannan lokacin mun damu matuka a kan irin barnar da annobar cutar Korona ta yi wanjen kara masu fama da talauci, da tsananin gurbacewar muhalli da kuma abubuwan da yakin Rasha da Yukrain ya haifar wa duniya da kuma yadda lamarin ya haifar da matsananciyar matsalar rashin abinci, a halin yanzu muna fuskantar karanci abinci mafi girma da aka taba fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu. Wadannan matsalolin sun kawo cikas ga hanyoyin samar da abinci a wasu lokutta hanyoyin samar da abincin sun kan kulle ne gaba daya, kuma gashi matsaliolin sai kara ta’azzara suke yi, al’umma da dama na cigaba da fuskantar rashin abinci, Talakawa ne suka fi fuskantar wannan matsalar domin kuwa wuraren samun abinci su duk sun bushe a inda kuma ake iya samun abinci yana da tsadar gaske.
A bayyane lamarin yake cewa, al’murra sun rude, iyalai da dama basa iya ciyar da kansu ba wai maganar cin abin mai gida jiki ba, a ma dai samu abinci da za a ci. Abin da ke faruwa sakamakon rashin cin abinci mai gina jiki shi ne cutar yunwa da cututtuka masu tsanani a cikin al’umma, wannan kuma ya fi tsanani ne a tsakanin yara kanana don kuwa karancin abinci ya zamma wani makami da ke cutar da yaran talakawa.
Yawan ‘yan Nijeriya da ke fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki da za su ci da rashin kayan sawa da kuma matsugunai yana karuwa ne a kullum garin Allah ya waye. Wannan abin talaici ne in aka lura da dimbin albarkatun kasa da Allah ya hore mana wannan sai dai ace babu cikkakiyar damuwa ne da rashin sanin yakamata.
Abin kura a kan lamarin talaucin da ake fuskantar Nijeriya shi ne na yadda a duk shedkara ake jin gwamnati na ware dimbin kudade da sunan yaki da talauci amma kuma al’amarin a kullum sai kara kazancewa yake yi.
Wannan Jaridar ta lura da cewa, duk ikirarin da wannan gwamnatin ke yi na cewa ta fitar da al’ummar Nijeriya fiye da Miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekara 10 amma har yanzu Nijeriya na nan rike da kambunta na hedikwatar talauci na duniya, inda ake da fiye da mutum miliyan 93.9 da ke rayuwa a cikin talauci.
Amma dai gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, shirin nan na fitar da mutum miliyan 100 daga kangin talauci zai tabbata ne daga shekarar 2030, inhar dukkan masu truwa da tsaki suka bayar da nasu gudummawar yadda yakamata. Wannan dai da kamar wuya, in har gwamnati ta kasa yakar cinhaci da rashawa wadda ke ta kara ta’azzara a kullum.
A shekarar 2019, gwamnatin tarayya ta yi watsi da wani rahoto inda aka ayyana Nijeriya a matsayin hedikwatar talauci a duniya duk kuwa da shugabannin duniya kamar Firayministan Birtaniya Theresa May, ta kara jaddada wannan matsayar. Daga baya an bayyana mana cewa, Shugaba Buhari zai mayar da hankali a yaki da talauci a zangonsa na biyu a ofis.
Amma a yanzu kusan saura wata 7 zuwa karshen wa’adinsa na biyuu amma babu wata kwakwarar hujja da ke nuna cewa, abubuwa sun inganta a kan yadda suke a shekarar 2019.
Maimakon haka ma al’ummura sun kara tabarbarewa ne, tun daga lamarin tsaro ga shi kuma matsalar ambaliyar ruwa da ta addabi sassan kasar nan na cigaba da wahalar da al’umma.
Tabbas za a iya magance talauci, ba bin da ba zai iya yiwuwa ba ne. daya daga cikin hanyoyin magance talaucin shi ne sanya talakawa a cikin tattauanwar fito da hanyoyin magance talaucin da kuma karfafa tattalin arziki da samar da hanyoyin aikin yi ga al’ummar Nijeriya, haka kuma dole a yi maganin banbancin da ake nunawa a tsakanin jinsin maza da mata, yana kuma matukar muhimmanci a inganta cibiyoyin al’umma, wannan tabbas zai matukar kawa karshen talauci a tsakanin al’ummar duniya gaba daya.
Muna kira ga gwamnatin tarayya ta tabbatar da sanya tsare-tsaren yaki da talauci a cikin tsarin ayyyukanta tare da kuma tabbatar da ana aiwatar da tsarin ba tare da bata lokaci ba, ta haka ‘yan Nijeriya da dama za su samu fita daga kangin talauci.
Haka kuma yakamata gwammati ta zuba jari a harkokin kasuwanci a yankunan karkara wanda ta haka al’umma gaba daya za su amfana