Bayan da aka fuskanci annobar cutar Korona ‘yan shekaru da suka gabata ga kuma yadda kyandar Biri take kara saurin yaduwa sai kuma ga labarin bullar wata kwayar cuta mai tada hankali al’ummar duniya da gaske dake musabbabin kamuwa da Marburg.
Ita wannan kwayar cutar Marburg data bulla a kasar Ghana yammacin Afirka kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bada sanarwar hakan.
- Sabon Fim din JAMILA Zai Fara Haskawa A Makon Nan –Hafsat Sa’eed
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Yara 3, Sun Bukaci Kudin Fansa Naira Miliyan 100 A Jihar Kogi
Mutane biyu wadanda basu da alaka da juna suka mutu bayan an gwada su an gano sun kamu da cutar a kudancin sashen Ashanti na kasar kamar dai yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana hakan, inda sakamakon gwajin da ma’aikatar lafiya ta yi ya nuna sun mutu ne sanadiyar cutar.
Cuta ce mai saurin yaduwa da kuma hadari tayi kama da cutar Ebola, wanda ya zuwa yanzu kuma ba wani rigakafin dake maganinta.
Jami’an lafiyar kasar sun yin iyakar kokarinsu wajen yin duk abubuwan da za su hana cutar yaduwa, yayin da hukumar lafiya ta duniya take taimakawa da jami’anta tare da kayan aiki zuwa kasar.
“Saurin daukar matakin da sahen kula da lafiya ya taimaka, ta yadda za a dakile yaduwar cutar, wannan shi ya dace domin da ace ba a dauki matakin ba, da cutar ta yi saurin yaduwa.
Darektan sashen na ofishin hukumar lafiya ta duniya dake kulawa da nahiyar Afirka Matshidiso Moeti ne ya bayyana hakan.
Abubuwan da suka kamata a sani dangane da kwayar cutar Marburg.
Marburg cuta ce wadda ta yi kama data Ebola wadda ta dade tana sanadiyar mutuwar mutane a yammacin Afirka shekaru masu yawa.
Jemagu masu bibiyar kayan marmari ke yada cutar ga mutane musamman ma wadanda suke aikin hadar ma’adinai.
Jemagun da suke dauke da kwayar cuta sune ke yada ta, kuma tafi cutar Ebola,sai dai masana ilmin kimiyya suna aiki tukuru domin hana yaduwar cuatar.
Da zarar mutum ya kamu da cutar ita kwayar cutar zata iya yaduwa cikin kankanen lokaci ta hanyar yaduwa ta wani abu mai ruwa-ruwa daga mutanen da suka kamu da ita, kamar Jini, Miyau da kuma Fitsari.
Kai har ma akan wasu abubuwa masu damsi kwayar cutar na iya makalewa.‘Yan’uwa da ma’aikatan lafiya sune wadanda za su fi saurin kamuwa da cutar, saboda kasancewar su da wanda ya kamu da cutar.