Kimanin mutune kusan ɗari (100) ne suka rasa rayukansu, sakamakon ɓullar cutar Sanƙarau (Meningitis) a wasu yankunan jihar Jigawa.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa akwai kuma kimanin mutane sama da 360 da suka kamu da cutar wadda mafi yawansu ƙananan yara ne da basu haura shekaru 15 da haihuwa ba.
Bincike ya tabbatar da cewa al’amarin ya fi ƙamari a wasu yankunan da ke da maƙwabtaka da ƙasar Nijer masu yanayi na zafi mai tsanani.
Wasu daga cikin yankunan da al’amarin ya faru sun haɗar da yankin Gumel, Maigatari, Sule-Tankarkar, Babura, Gwiwa da sauran wasu yankin na arewacin jihar.
LEADERSHIP Hausa ta yi tattaki zuwa wasu yankunan da al’amarin ya shafa inda iyalan wasu da suka rasa ‘yan’uwansu suka tabbatar da barnar da cutar ta sankarau a yankinsu.