A duk lokacin da ruwan sama ya fara sauka, mutane da dama kan fuskanci matsalolin rashin lafiya iri daban-daban.
Amma wadane irin cututtuka ne suka fi yaduwa a wannan lokaci na damina, sannan kuma yaya za a kare kai da iyali daga kamuwa da cututtukan?
- APC: Ko Sadaukarwar Ganduje Za Ta Dakile Barazanar Jam’iyyun Adawa A Zaben 2027?
- Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar
Wani likita, mai suna Dakta Ahmad ya lissafo cututtukan da suka fi yaduwa a wannan lokaci na damina kamar haka:
– Zazzabin cizon sauro (Maleriya): Zazzabin cizon sauro, shi ne jagoran cututtukan da aka fi fama da su a lokacin damina.
A duk lokacin da ruwa ya fara taruwa a kwatoci da shara, sauro na samun damar hayayyafa cikin sauki, wanda hakan kan kasance a matsayin barazana, musamman ga yara da kuma mata masu juna biyu.
“A kowane mako, muna karbar yara fiye da 100 da ke fama da cutar maleriya. Sannan kuma, mafi yawancin lokaci; ba a kawo su asibiti, sai cutar ta tsananta”, in ji likitan.
– Ciwon ciki da amai da gudawa (kwalera): Lokacin damina na kawo yawan samun gurbataccen ruwa, wanda ke haddasa cututtuka kamar ciwon ciki, amai da gudawa da kuma zazzabin taifod.
Wannan na yawan shafar yara, musamman ‘yan kasa da shekara biyar.
Dakta Ahmad ya kara da cewa, “Yara na da rauni a garkuwar jikinsu, sannan kuma idan suka kamu da gudawa, jikin nasu na rasa ruwa cikin sauri, har ta kai ga samun mace-mace.”
-Kaikayi da kurajen fata: Likitan ya ce, lokacin damina na matukar kawo danshi, wanda ke haddasa kaikayi da tabo-tabo a fata da gashi da kuraje, wanda ke yaduwa cikin yara da kuma matasa.
“Mafi yawan yara da manya da ke zuwa asibiti a lokacin damina, suna fama da kaikayin fata da kuraje ne a jiki”, a cewar Dakta Ahmad.
– Mura da tari da ciwon makogwaro: Sanyin damina da iska mai danshi, na haddasa mura da tari, musamman ga yara da kuma tsofaffi.
Yana iya haifar da matsanancin ciwon makogwaro da kamuwa da cututtukan numfashi kamar ‘pneumonia’.
“Yara da manyan da ba su da rigar sanyi ko suna yawan shan ruwan sanyi a lokacin damina, na iya fara tari da hanci mai yoyon majina”, in ji likitan.
– Ciwon Ido (Apollo – Conjunctibitis): Ciwon ido na ‘Apollo’ na yaduwa sosai a lokacin damina. Idanu sukan yi ja, su kumbura, su rika zubar da ruwa, suna kuma yin zafi.
“Ciwon ‘Apollo’, na yaduwa ne ta hanyar hannu da kuma amfani da kayayyaki irin su tawul ko gado tare da mai cutar”, likitan ya kara bayyanawa.
Ga Alamomin Wadannan Cututtuka Kamar Haka:
Alamomin zazzabin cizon sauro:
Zazzabi mai tsanani
zafin jiki
Jin sanyi da zufa
Ciwon kai da kaikayin jiki
Yawan gajiya
Alamomin Ciwon Ciki Da Amai Da Gudawa (Kwalera):
Yawan zuwa bayan gida
Ciwon ciki
Aman da ya ki tsayawa
Rashin karfi da gajiya
Bushewar baki da fata
Alamomin kurajen fata da kaikayi
Kaikayi da kalar ja a fata
Kuraje na yin tsiro a kan fata har wasu suna ruwa da fashewa
Saurin fushi ko kukan yara saboda jin zafi
Alamomin mura da tari da ciwon makogwaro
Tari da mura
Zafi a makogwaro
Toshewar hanci
Yawan nishi da jin nauyi a kirji
Alamomin Ciwon Ido (Apollo – Conjunctibitis):
Jan ido da kumburi
Zubar da ruwa ko kwantsa daga ido
Jin kaikayi a ido
Matakan Kariya:
Matakan Kariya Daga Zazzabin Cizon Sauro:
– Amfani da gidan sauro da aka shafa wa magani
– Kawar da ruwa da shara a kusa da gida
– Feshe wurin barci da maganin sauro
– Guje wa fita da dare ba tare da tufafin da ke rufe jiki ba
Matakan Kariya Daga Ciwon Ciki Da Amai Da Gudawa (Kwalera):
-Tafasa ko tace ruwan sha
-Guje wa shan ruwa daga rafi ko rijiya mara rufi
-Wanke hannu da sabulu kafin cin abinci da bayan-gida
-Rage cin abinci daga titi ko inda ba a san yanayin tsaftarsu ba
Matakan Kariya Daga Kurajen Fata Da Kaiƙayi:
– Wanka da ruwa mai tsafta sau biyu a rana
– Busar da jiki sosai bayan wanka
– Gujewa saka kaya masu nauyi ko wadanda ke dame fata
Kar a rika amfani da tawul, soso ko man jiki tare da wani.
Matakan Kariya Daga Mura Da Tari Da Ciwon Makogwaro:
-Sanya rigar sanyi, musamman da dare
-Shan ruwa mai dumi da shayi
-Guje wa zama cikin iska
-Kula da tsaftar hanci da baki
Matakan Kariya Daga Ciwon Ido (Apollo-Conjunctibitis):
– Wanke hannu akai-akai
– Gujewa taba ido da hannu mara tsafta
-Kar a rika amfani da mayukan ido ko tawul na wani
– A nisanci wanda ke dauke da ciwon ido, har sai ya warke
– Lokacin damina lokaci ne da ke dauke da albarka, amma a lokacin guda kuma cike da hadari ga lafiyar Dan’adam.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp