Wani Ginin Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguzo ɗazu-ɗazun nan a kan Titin Unity da ke Kasuwar Kantin Kwari
Wakilinmu ya ruwaito mana cewa ana fargabar mutum guda ya rasa ransa a benen.
Tuni jami’an kwana-kwana da ‘yan sanda suka kai agaji wajen benen da lamarin ya faru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp