Gwamnatin tarayya ta bullo da dabarar yadda za ta ci gajiyar dala tiriliyan bakwai na kayayyakin kasuwancin Musulunci na duniya.
Babban mai taimaka wa shugaban kasa kan inganta fitar da kayayyaki a ofishin mataimakin shugaba kasa, Mista Aliyu Sheriff, shi ne ya sanar da hakan kamar yadda yake kunshe a cikin sanarwar da kakakin mataimakin shugaban kasa, Mista Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
- Kwangilar Biliyan 30: PDP Ta Bukaci EFCC Ta Binciki Gwamnatin Sakkwato
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 A Birnin Gwari Da Giwa Bayan KuÉ“utar Da Mutane 20Â
Sheriff ya ce a cikin yunkurin cimma wannan dabarar, gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta kaddamar da cikakken tsarin yadda Nijeriya za ta shiga a dama da ita a bangaren tattalin arzikin Halal.
A cewar babban hadimin shirin, na daga cikin manufofin kyautata tattalin arziki ta hanyar kasuwar Halal wacce ta dace da manufofin musulunci da kuma da’a da na mutuncin duniya.
Sheriff ya ce shirin zai hada kan hukumomin gwamnati, masu zaman kansu da kungiyoyin na kasashen waje ta yadda za a kyautata da bai wa Nijeriya damar shiga a dama da ita a kasuwar tattali arziki ya Halal na duniya.
“Tattalin arzikin Halal na nuni da nasarorin da aka samu na damarmakin Nijeriya wajen bunkasa tattalin arziki, samar da musayar canji na kasa da kasa da kuma cimma manufar ci gaba mai daurewa.
“Ta hanyar kara fitar da kayayyakin Halal zuwa kasashen waje da kuma mai da hankali kan sauya shigo da kayayyaki, za mu kai ga aiwatar da karin kusan dala biliyan 1.5 na kudaden shigarmu nan da shekarar 2027,” in ji Sheriff.