Rundunar sojojin hadin gwiwa ta ‘Operation Hadin Kai’ a yankin Arewa maso Gabas ta haramta amfani da jirage marasa matuka (UAV), a yankin.
Kwamandan Rundunar Sojan Sama, Air Commodore UU.Idris, wanda ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa da ya fitar, ya ce amfani da jirage marasa matuka ba tare da izini ba yana haifar da barazana a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
- ‘Yan Boko Haram 120,000 Da Suka Miƙa Wuya, Fiye Da 60,000 Yara Ne – CDS
- Dakarun MNJTF Sun Daƙile Harin Da Aka Kai Sansanin Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10 A Kamaru
Ya koka da cewa, hukumomin gwamnati da masu zaman kansu suna sarrafa jiragen ba tare da amincewar Sashin rundunar sojin sama ta ‘Operation Hadin Kai’ ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Yawaitar jirage marasa matuka don harkokin cikin gida na haifar da babbar barazana ga tsaro.
“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ke sarrafa wadannan jirage marasa matuka ba tare da la’akari da wasu ka’idoji kan ayyukansu ba.
” Har ila yau, a ranar 7 ga watan Janairun 2025, an kama wani fasinja a wani jirgin sama mai zaman kansa daga Maiduguri zuwa Monguno dauke da wani jirgi mara matuki a wani bincike da ake yi a jirgin.”
Don haka, ana tsoron kar masu tada zaune tsaye su fara amfani da shi wurin leken asiri da kai hare-hare kan al’ummomin da ba su ji ba su gani ba