Labarin da muke samu da ɗumi-ɗuminsa ya bayyana cewa a jiya da dare da misalin ƙarfe 10, ‘yan bindiga sun auka gidan Sarkin Kagarko mai daraja ta biyu da ke Kudancin Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu iyalansa.
Majiyarmu daga garin na Kagarko ta bayyana mana cewa, daga cikin waɗanda aka tafi da su akwai matar sarkin guda ɗaya, sai kuma matan ‘ya’yansa da jikoki.
Majiyar ta ƙara da cewa, sun yi yunƙurin tafiya da mai martaba sarkin, “suka ce masa ya tashi su tafi, sai ya ce musu ba shi da ƙoshin lafiya, sai suka ce za su kashe shi, sai ya ce musu ai dama abin da yake jira kenan. To, daga nan ne suka ƙyale shi.” In ji majiyar.
Har ila yau, majiyar ta ce an ɗauki tsawon lokaci ‘yan bindigar suna cin karensu ba babbaka a gidan sarkin ba tare da an kawo ɗauki ba daga jami’an tsaro.
Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin Sakataren Masarautar Kagarko, Malam Yahaya Ibrahim, sai dai ya ce suna shirin fitar da sanarwar manema labarai dangane da lamarin.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai babu wata sanarwa game da lamarin daga Rundunar ‘Yansandan Jihar Kaduna.
A kwanan nan dai ‘yan bindiga na ƙara zafafa hare-haren da suke kaiwa a yankin Ƙaramar Hukumar Kagarko da ke Kudancin Jihar Kaduna, inda ko a ‘yan kwanakin da suka gabata, sun tarwatsa wasu ƙauyuka da ke gabashin garin Kagarko musamman ƙauyen Janjala.
Kana sojoji sun yi dirar mikiya a garin na Kagarko a makon da ya gabata inda suka damƙe wasu da ake zargin masu yi wa ‘yan bindigar leƙen asiri ne.
Waɗanda aka kaman, sun jagoranci sojojin zuwa cafke ƙarin wasu masu yi wa ‘yan bindigar leƙen asiri a ƙauyen Janjala ciki har da Madakin Janjala inda ake ci gaba da bincike a kansu.
Wannan ya sa wasu ke hasashen ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Sarkin na Kagarko ne domin ɗaukar fansa. Amma dai sakamakon bincike ne zai tantance hakan.