Da sanyin safiyar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki wani bankin yanki mai suna Lapo da ke Lokogoma a yankin Phase II a Lokoja a Jihar Kogi, inda suka sace wasu kudade da ba a tantance ba.
Wani ma’aikacin bankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan fashin inda suka kutsa ta taga da silin, suka fasa rumbun ajiya suka tafi da kudaden.
- Da Ɗumi-ɗuminsa: ‘Yan Bindiga Sun Afka Gidan Sarkin Kagarko A Kudancin Kaduna, Sun Tafi Da Iyalansa
- Buhari Ya Yi Duk Abin Da Ya Dace Wajen Magance Matsalolin Nijeriya – Shagalinku
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya ce “Al’amarin ya faru ne na fasa gidaje da sata. Barayin sun kwashe kudi har N21,910.”
Talla