Rahotanni sun bayyana cewa, gobara ta tashi a gidan gwamnatin jihar Katsina a safiyar yau Litinin.
Sai dai har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
- Komawar Ronaldo Saudiyya: Riba Ko Faduwa Ga Al-Nassr?
- Hamas: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Isra’ila Saboda Ƙin Amincewar Ƙasar Kan Tsagaita Buɗe Wuta
Wata majiya da ke kusa da gidan gwamnati, a Katsina ta shaida cewa, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safe.
Kokarin jin ta bakin Babban sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahim l Mohammed, ya ci tura har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton
Cikakkun bayanai daga baya…