Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da rasuwar mataimakin shugaban Ma’aikatansa, Gboyega Soyannwo, a ranar Laraba yana mai shekaru 55.
Sanwo-Olu, wanda ya jajanta wa iyalan Soyannwo a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce, mutuwar babban hadimin nasa ta kasance kwatsam kuma mummunan labari a wajensa.
- Ƙungiyar Ƙwadago Ta Yi Fatali Da Tayin Naira 48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
- ‘Yansanda Sun Kama Matashin Da Ya Cinna Wa Masallaci Wuta A Kano
Ya bayyana marigayin a matsayin amintaccen dan uwa da ya bada gaskiya wajen bunkasar Legas.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ina mai matukar bakin cikin sanar da rasuwar mataimakin shugaban Ma’aikatana, Gboyega Soyannwo. labarin tafiyar Gboyega ta ɗimautani.
“Gboyega ba wai mataimakin shugaban ma’aikata na ne kadai ba; Ya kasance ɗan’uwana, amintacce kuma mai imani da burinmu na gaba ɗaya ga Legas.
“Ba za a taba mantawa da sadaukarwar da ya yi ga jihar Legas ba. Ina mika ta’aziya ta ga matarsa Yewande da ‘ya’yansu a wannan mawuyacin lokaci.”