Wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a Kusogbogi dake karamar hukumar Agaie a jihar Neja.
Daily trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a iyakar da ke tsakanin kananan hukumomin Agaie da Lapai.
- Bikin Bazara Na Duniya Ne
- An Kammala Gwaje-Gwajen Wasan Kwaikwayo Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG Na 2025
Majiyoyi sun shaida cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na safiyar ranar Talata amma ba a samu asarar rai ba.
Wani mazaunin Lapai, Malam Mahmud Abubakar, ya ce tankar ta yi hatsari ne kuma ta kone kurmus yayin da take kokarin wuce wata babbar mota.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp