Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Yankin Sabon Garin Nassarawa -Tirkaniya da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna yau Litinin 3 ga Afrilu, 2023.
Bayanan hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Samuel Aruwan.
A cewarsa, an cimma wannan matsayar ce biyo bayan tabarbarewar doka da oda da ta kai ga kashe wasu mutane biyu a wani rikici da ya barke a Unguwar.
A halin da ake ciki, an umurci hukumomin tsaro da su aiwatar da dokar ta-baci a wurin da aka ayyana, domin maido da doka da oda yayin da ake ci gaba da bincike.
Hakazalika, an yi kira ga jama’ar yankin da su kiyaye bin dokar ta hana fita wanda za ta fara aiki nan take.
Kana ana sa ran Gwamnatin Jihar Kaduna za ta sanar da duk wani karin bayani nan gaba kadan idan akwai bukatar hakan, in ji sanarwar.