Jami’yyar APC a Jihar Zamfara ta kori dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar kananan Hukumomi birnin Magaji da Kauran Namoda, Hon. Aminu Sani Jaji.
Sakataren yada labaran jam’iyyar, Yusuf Idris ne, ya bayyana haka ga manema labarai a yau Juma’a a hedikwatar jam’iyyar da ke Gusau.
- Tinubu Ya Kaddamar Da Gangami Yakin Neman Ilimi
- Hajjin Bana: Hawa Da Gangarar Da Maniyyatan Nijeriya Suka Sha Kafin Fara Tashi
A cewarsa jam’iyyar ta karbi koken dan majalisar ne daga mazabarsa kuma shugabanin karamar hukuma suka tabbatar da laifin da dan majalisar ya aikita, suka kawo wa jami’yyar a matakin jiha domin ta yi bincike.
Bayan tabbatar da laifin kwamitin zartarwa na jiha, karkashin shugaban jam’iyyar, Tukur Da Fulani da sa hannun sakataren jam’iyyar Ibrahim Dan Galadiman Birnin Magaji suka zartar da hukuncin.
Idris ya bayyana kadan daga cikin manyan laifukan da dan majalisar ya aikata wa jami’yyar wanda ya sanya dole suka dakatar da shi.
“A lokacin babban zaben da ya gabata ya yi wa jami’yya zagon kasa a mazabu uku da ba a yi zabe ba.
“Baya mutunta shugabannin jami’yya na mazabarsa da na karamar hukumarsa, kuma yana gudanar da taruka ba tare da izinin jami’yya ba da dai sauransu,” in ji sakataren yada labaran jam’iyyar a jihar.