A yayin da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta kaddamar da fara aikin jigilar maniyyatan bana daga Jihar Kebbi inda maniyyata 428 suka tashi a ranar Laraba daga filin tashin jirage na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi babban birnin Jihar Kebbi, alhazai da dama ne suka kasa cika kudaden aikin hajin bana saboda yadda ya yi tashin gwauron zabo sakamakon hauhawar farashin Dala, abin da aka ba a taba gani ba a tarihin zuwa aikin hajji a kasar nan.
Wannan yana faruwa ne saboda yadda darajar naira ta karye dala kuma ta yi tashin da ba a taba gani ba a tarihin Nijeriya.
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Yi Taron Manema Labarai Na Hadin Gwiwa
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
Jadawalin hukumar alhazai ya nuna cewa, mafi karancin kudin zuwa aiki hajji na wannan shekarar shi ne naira miliyan 4 wannan karin kudin ya sa maniyyata da dama ba su iya cika kudaden ba. Haka ya sa aka samu mutum 65,047 kawai ne za su sauke farali a bana koma bayan sauran shekaru inda ake samun mutum har kusan dubu dari.
Farashin kujerar zuwa aikin hajji a wannan shekara kamar yadda mataimakiyar daraktar watsa labarai a hukumar alhazai NAHCON, Hajiya Fatima Sanda-Usara, ta sanar ya nuna cewa an samu karin Naira miliyan 1, 918,032.91 a kudin zuwa aikin hajin 2024 inda a halin yanzu maniyyata suka biya Naira miliyan 6.8. wanann karin ya jefa miniyyata da dama cikin rudu, dubban maniyyata sun rasa kujerar su saboda karin da aka yi daga bayan nan. Wannan kuma yana faruwa ne saboda karyewar darajar naira da kuma hauhawar farashin dala kamar yadda Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa, Malam Jalal Ahmed Arabi ya sanar a tattaunawarsa da manema labarai kwanakin baya.
Tsoron da ake yi kuma shi ne in har Nijeriya bata iya cike adadin kujerun da aka ayyana mata ba tana iya asarar wasu kujeru a shekaru masu zuwa. Kasar Saudiya ta ayyana wa Nijeriya kujeru 95,000 a hajjin bana inda aka warewa jihohin arewa kujeru 75,000 kamfanonin jigilar mahajjata kuma aka basu kujeru 20,000.
Wannan ya sa masu ruwa da tsaki suka zafafa kira ga gwamnatocin jihohi musamman masu yawan maniyyata su kawo wa maniyyatan jihohinsu tallafin ganin sun samu daman gudanar da aikin hajji. Tabbas wannan kira ya samu karbuwa a wasu jihohi inda wasu gwamnoni suka bayar da tallafi na musamman don rage wa maniyyata kudin zuwa aikin hajjin bana.
Rashin cika kujerun da kasar saudiya ta ayyana wa Nijeriya zai iya kai ga rage wa Nijeriya yawan kujerunta a shekaru masu zuwa, wannan kuma wani abu ne da zai iya jawo wa Nijeriya koma baya musamman ganin Nijeriya ce kasa ta uku na yawan alhazai a duniya kuma kasa ta daya a Afrika.
Wadannan dalilan ya sa NAHCO ta zafafa kira domin a kawo alhazan dauki. Yawan alhazan da aka raba a tsakanin jihohin kasar sun kasance kamar haka Adamawa 1,642; Borno 1,780; Taraba 950; Yobe 1,120; Bauchi 2,315; Benue 87; Ekiti 186; FCT. 2,491; Gombe 1,373 sai kuma Jigawa da ke da maniyyata 1,250.
Sauran kuma sun hada da Jihar Kaduna da take alhazai da suka fi yawa- 4,493 sai Kano – 3,057; Katsina 2,654; Kebbi 3,419; Kogi 13; Kwara 3,000; Nasarawa 1,866; Neja 3,201; Ondo 491; Filato 1,126; Sakkwato 3,643 and Zamfara 1,596.
Haka kuma Jihar Bayelsa nada maniyyata 13; Delta – 36, Ribers – 47, Ebonyi – 13, Edo – 295, Enugu – 18, Imo – 100; Legas kuma nada maniyyata 1, 861; Ogun, 925; Osun 1,590; Oyo 1,047; sai kuma bangaren jami’an tsaro da aka ware musu kujera 365; HSS – 1884 saura an ware musu kujera – 1,500. Yayin da jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra da Kross Ribas basu da maniyyataci ko daya.
Wakilanmu na jihohi sun nakalto mana irin tallafin da gwamnoni suka ba maniyyata da kuma wadanda suka yi alkawarin tallafa wa maniyyata in an isa kasa mai tsari domin rage musu tsadar da aka fuskanta na kujerar hajjin bana,
Jihar Kano
Kowane Maniyyati Ya Samu Tallafi 500,000.00 Daga Gwamnati
A kokarin da yake na ganin mahajjjatan Jihar Kano da suke fatan sauke faralin wannan shekarar, Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gwangwaje Maniyyatan Jihar 3,000 inda ya tallafa wa kowane Alhaji da gudunmawar Naira dubu dari biyar-biyar domin samun saukin cika kudin kujerar aikin hajji bana
Gwamna ya bayyana wannan tallafi ne sakamakon karin kudin kujerar aikin hajji bana wadda ta samu karin da yasa har wasu maniyyata ke ganin ba zasu iya samun cikon kudin kujerar ba. Hakan tasa a tausayi da kishin irin nasa, yaga da cewar kawowa wadannan alhazai ‘yan asalin Jihar Kano saukin gaggawa inda ya Rabawa kowa nen su kyautar Naira dubu 500,000.00.
Haka kuma yana daga cikin kyawawan manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf ana sa ran wasu Alhairan za su biyo baya wanda Maniyyatan Kano za su yi hafzi dasu, baya ga kyakkyawan kokarin da hukumar Alhazan Kano ta yi na samawa alhazan Jihar Kano masauki kusa da harami.
Haka kuma gwamnan jihar Kanom, Abba Kabir Yusuf ya amince da karin kudin goron sallah da gwamnatin ke bai wa alhazai duk shekara, yanzu za a ba alhazan jihar Kano goron sallah na SR 100 daga DSR 50 dab ke bayarwa a shkarun baya wanna ya nuna an yi karin kasha 100 kenan, z araba wa dukkan maniyyata 3,110 daga jihar. Shugababn hukumarb jin dadin alhazan jihar Laminu Rabi’u Danbappa ya asanar da haka a taron masu ruwa da tsaki na aikin hajjin bana da aka yi otal din Central da ke kano ranar Litinin. A kan haka ya nemi alhazai su yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya.
Jihar Kebbi
Kowanne Maniyyaci Ya Samu Tallafin Naira Miliyan 2 A Jihar Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta biya wa Naira miliyan 1 ga kowane mahajjata 3,344 da ke da niyyar zuwa aikin Hajjin bana daga jihar, Naira Miliyan 1 wanda biyan Naira Miliyan 1 daga gwamnatin jihar ya biyo bayan karin kudin kujerar hajji da ya kai kimanin Naira miliyan biyu da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sanar.
An cimma wannan matsaya ne a taron majalisar zartarwa na gaggawa wanda mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida ya jagoranta a Birnin Kebbi.
Da yake karin haske ga manema labarai game da sakamakon taron, kwamishinan yada labarai da al’adu na, Alhaji Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin kara daukaka martabar Gwamna Nasir Idris na ganin an kiyaye dabi’un addini domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
Ya bayyana cewa an tsara kudin da aka baiwa kowane mahajjaci ne domin a samu saukin biyan kudin aikin hajji gaba daya kafin ranar rufewa.
“A cikin kimanin Naira miliyan 2 da NAHCON ta nema a matsayin karin kudin tafiya, gwamnatin Jihar Kebbi ta sanya wa kowane mahajjaci Naira miliyan 1 yayin da sauran mahajjata za su biya domin su kammala biyansu”.
“Alhazan da suka kammala biyan kudin tafiya suma za su ci gajiyar Naira miliyan 1 daga gwamnati,” in ji Kwamishinan.
Zamfara
Gwamnan Zamfara Mayar Wa Da Alhazai Naira Miliyan 747 Da Ya Makale A Shekarun Baya
A shirye-shirye da Hukumar Alhazan Jihar Zamfara ke yi na aikin hajin bana. A yanzu gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta biya sama da naira Miliyan dari bakwai da ar’bain da bakwai na kudin Mahajata da suka biya a bara da gwamnatin da ta shede ta cinye kudaden nasu.
Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar Alhazai, Ibrahim Gidan Tsaka ne ya bayyana wa wakilinmu a lokacin da ya ke tattaunawa da shi.
Gidan Tsaka ya bayyana cewa, gwamnatin Zamfara ta yi na mijin kokarin biyan kudin ga mahajatan da aka cinye kudaden su Kuma cikin kudurar Allah za su samu sauke farali a bana.
Kuma Hukumar Alhazai ta mika wa Gwamna Dauda Lawal bukatunta da kuma Tallafin da alhazai ke bukata ga gwamnatin Jihar kuma da yardar Allah mun san gwamna zai biya mana bukatun, kafin nan da lokacin tashin Alhazan mu.
Borno Da Yobe
Maniyyata A Borno Da Yobe Ba Su Samu Wani Tallafi Ba
Sakamakon karin kudin kujerar aikin Hajjin bana (2024) wanda Hukumar Alhazan Nijeriya a kwanakin baya ta ayyana, karin na kimanin Naira miliyan daya da dubu dari tara, yayin da kudin kujerar ya koma naira miliyan shida da dubu 800.
Hukumar ta bayyana daukar wannan matakin ne biyo bayan tashin gwauron zabi da musayar kudade da Dalar Amurka ya haifar yayin da matakin ya sanyaya gwiwoyin maniyata da yawa, al’amarin da ya sanya gwamnatocin wasu jihohi baiwa maniyatansu tallafin kudaden da za su cike gibin da aka samu a wannan shekara.
Duk da wannan matakin wasu jihohin, amma gwamnatocin Borno da Yobe ba su yi wani abu ba a kan wannan batu dangane da tallafa wa maniyatansu.
A zantawar wakilinmu da wasu maniyata a jihar Yobe; Malama Safiyyat Muhammad Damaturu, ta bayyana cewa sun kammala shirin tafiya aikin Hajjin bana, bayan sun biya dukkan kudaden da Hukumar Alhazan ta bayyana, ba tare da samun tallafin ko sisin-kwabo ba.
“Amma gwamnati ta ce wai za ta biya mana kudin Hadaya, idan mun je Makka. Amma zancen tallafin karin kudin kujerar har yanzu ba mu wani abu a kai ba.” Ta bayyana.
A zantawar wakilinmu da yayi da Shugaban Hukumar Alhazan jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya ce har yanzu babu wani zancen baiwa maniyatan jihar Yobe wani tallafi, sakamakon karin da aka samu na kudin aikin Hajjin bana.
A Borno, majiyoyi daban-daban masu karfafa juna sun bayyana cewa babu wani tallafi a hukumance da gwamnatin jihar ta ayyana dangane da baiwa maniyatan jihar wani tallafi na bai-daya. Amma majiyar da ba ta hukuma ba ta ce maniyatan da suka biya kudi kafin a samu karin sun samu tallafin.
Duk kokarin jin ta bakin Shugaban Hukumar Alhazan jihar ko wani jami’in gwamnati, abin ya ci tura.
Bauchi da Gombe
Maniyyata Sun Samu Tallafi Mai Tsoka
A Jihar Bauchi domin ganin an saukaka wa maniyyata a wannan aikin hajji na bana, gwamnatin jihar Bauchi a karkashin jagorancin Sanata Bala Muhammad ta tallafa wajen biyan kaso hamsin cikin dari na karin kudin kujerar aikin hajji da hukumar kula da alhazai ta yi ga maniyyata aikin hajjin bana.
Inda gwamnan ya sanar da biyan kashi hamsin cikin naira miliyan 1,918,000 na karin kudin hajji da NAHCON ta yi kan kowace kujerar zuwa aikin hajji. Maniyyata 1652 ne za su amfana, inda kowani maniyyaci zai ci gajiyar tallafin naira dubu N950, 000.
Idan za a tuna dai, hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa NAHCON, ta sanar da cewa, kowani maniyyacin da ya biya kudin kujera da niyyar sauke farali zuwa kasa mai tsarki a watannin baya, yanzu zai sake biyan naira miliyan 1.9 domin ya cike naira miliyan 4.9 da suka biya da zai zama sama da naira miliyan shida a matsayin kudin kujerar aikin hajjin 2024.
Kwamishinan kula da harkokin addinai na jihar Bauchi, Hon. Yakubu Hamza, shi ne ya sanar da matakin karin a wani taron manema labarai da ya kira a kwanakin baya, inda ya ce, adadin naira N1, 584, 268, 000 ne gwamnan ya biya wajen tallafa wa karin kudin kujerar ga alhazan.
Hamza ya ce wannan abun yabawa ne lura da cewa kudin da aka kara wa alhazan ba kowa zai iya cikawa ba, inda ya shawarci maniyyatan da su nemo rabin kudin su cika domin amfana da tallafin rabi da gwamnan ya musu.
Ya kara da cewa, wannan tallafin kaso hamsin ya hada har da alhazan da gwamnatin jihar ta dauki nauyin aikin hajjinsu, ya ce idan aka hada dukkanin alhazan da suka biya kudin kujera da fari da wanda da gwamnatin jihar ta biya musu, tallafin da gwamnan ya kara zai kai naira N2, 196, 110, 000.
Shi kuma a nasa bangaren, shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai na jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya ce, a kowani lokaci gwamna Bala na maida hankali wajen kyautata jin dadi da walwalar maniyyatan jihar.
Ya ce akwai wasu tsare-tsare da aka yi da za su tabbatar da kyautatawa maniyyata tare da jin dadinsu a yayin gudanar da aikin hajji na bana.
Haka zancen yake a jihar Gombe inda Gwamnan Jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da bada tallafin Naira 500,000 ga kowane mahajjacin jihar daga cikin maniyata 1,373 da za su yi aikin Hajjin bana.
Amincewar ta zo ne biyo bayan sanarwar da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta fitar a baya-bayan nan game da sauye-sauyen da aka samu a kudin Hajjin bana.
Inuwa Yahaya ya ce an bada tallafin ne don ragewa maniyata radadin kalubalen halin da suka tsinci kansu biyo bayan karin kudin hajjin bana.
Wannna bayanin dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya fitar ga manema labarai.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi fatan wannan tallafi zai taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin bana cikin tsanaki, tare da inganta jin dadin maniyyatan Jihar Gombe dama samar musu yanayi mai kyau na gudanar da ayyukan addini duk da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi.