Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashin ma’aikata daga kashi 25 zuwa 35 na ma’aikatan tarayya.
Tsarin albashin ya hada da ma’aikata (CONPSS), albashin cibiyoyin bincike (CONRAISS), albashin ‘yansanda (CONPOSS), albashin sojoji (CONPASS) da sauransu.
- ‘Yar Sanda Da Wata Sun Shiga Hannu Kan Sato Yara 5 Daga Sakkwato
- Gwamnati Na Buƙatar Dala Biliyan 10 Don Farfaɗo Da Ɓangaren Wutar Lantarki
Idan dai ba a manta ba, tuni wadanda ke cikin manyan makarantun harkokin kiwon lafiya suka samu karin albashinsu da sauran ma’aikatan Jami’o’i.
Kwalejojin kimiyya da fasaha da na ilimi, karin albashinsu na karkashin tsarin CONOCASS.
Sashen kiwon lafiya, su sun samu tagomashin karin albashin a tsarin CONMESS.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban jami’in yada labarai na hukumar kula da albashin ma’aikata ta kasa (NSIWC), Emmanuel Njoku, a ranar Talata, ta ce karin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun, 2024.
Gwamnatin Tarayya ta kuma amince da karin kudin fansho daga kashi 20 zuwa 28 ga masu karbar fansho, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun, 2024.
Sanarwar na zuwa ne a jajibirin ranar ma’aikata ta 2024.