Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana dan takarar (APC), Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban hukumar INEC kuma babban baturen tattara sakamakon zaben na kasa baki daya, Farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya ayyana Bola a cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa da ke Abuja a safiyar Larabar nan.
Ya ce, Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu kuri’u mafi rinjaye da aka kada kuma bisa cika dukkanin sharudda da ka’idojin doka hakan ya tabbatar da shi a matsayin Zabebben Shugaban.
Tinubu ya doke abokan karawarsa da kuri’u 8,805,655, inda mai biye da shi na (PDP), Atiku Abubakar, ya samu kuri’u 6,984,520.
Wanda ke biye da Atiku Abubakar a matsayin na uku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya samu kuri’u 6,098,798. Kazalika Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya samu kuri’u 1,496,687 kacal.
LEADERSHIP ta labarto cewa jam’iyyun siyasa 18 ne suka shiga aka fafata neman sa’a da su a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, wanda shi ne zaben shugaban kasa karo na 7 a wannan jamhuriyya ta 4 tun lokacin da aka dawo mulkin demokuradiyya a 1999.