Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta dage zaben Sanatan Enugu ta Gabas wanda za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris tare da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
Zaben, kamar sauran zabukan ‘yan majalisar dattawa, an shirya gudanar da shi gobe 25 ga watan Fabrairu.
- Nijeriya Ta Samu Raguwar Kudaden Shiga Da Kashi 3.10 A 2022 –NBS
- Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Kasafta Naira Biliyan 750.17 A Janairu
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya sanar da dage zaben a wani taro da aka yi a Abua ranar Juma’a.
Ya ce an dage zaben ne saboda kashe dan takarar Sanata na jam’iyyar Labour Party, Oyibo Chukwu, a ranar Laraba.
Leadership Hausa ta ruwaito yadda aka kashe Mista Chukwu a yammacin Laraba tare da wasu magoya bayansa biyar da ke cikin motarsa.
Mista Yakubu ya ce za a iya ci gaba da yakin neman zabe a yankin dan majalisar har zuwa sa’o’i 24 kafin zaben da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.
“Ina sa ran jam’iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani a mako mai zuwa,” in ji shi.
“Kamfen din da ya kare a daren jiya shi ne na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya ba na zaben jihohi da na majalisun dokoki ba.”