Kakakin Majalisar Dokokin jihar Zamfara ya fadi a zaben dan majalisa mai neman wakiltar mazabar Zurmi ta Gabas, Rt. Hon. Nasiru Maazu Maharya da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata.
Da yake sanar da sakamakon zaben mazabar ta Zurmi, malamin zabe zaben, Mudasiru Samaila, ya ce, Kakakin Majalisar Maazu ya samu kuri’u 13,820 ne a zaben da aka gudanar.
- INEC Ta Lashi Takobin Yin Nazari Kan Daukacin Almundahar ZabeÂ
- Jakadiyar Birtaniya A Nijeriya Ta Janye Taya Binani Murnar Lashe Zaben Adamawa
Inda takwaransa dan takarar kujerar Majalisar a karkashin jam’iyyar PDP, Bello Muhammed, ya samu kuri’u 21,197.
Don haka dan takarar Jam’iyyar PDP ya samu nasara a kujerar Majalisar dokoki mai wakiltar Zurmi ta gabas.
Kazalika, shi ma mataimakin Kakakin Majalisar na Jihar Zamfara, Hon. Musa Bawa, dan takara Jam’iyyar APC na Majalisar mai neman wakiltar mazabar Tsafe ta yamma shi ma ya fadi a zaben ba ya samu kuri’u 9,532.
Wanda ya lashe zabe a mazabar shi ne, Bilyaminu Samaila, na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 11,213.
Dan takara Jam’iyyar PDP ne ya samu nasarar lashe kujerar Majalisar dokoki mai wakiltar Tsafe ta yamma,” Inji Baturen zaben.