Mai shari’a Eleoje Enenche na wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin ya zartar da hukunci kan dakatar da gwamnatin tarayya da wasu bankunan kasuwanci 27 karawa ko yin katsalanda akan ranar 10 ga watan Fabrairu ko kuma bayar da duk wani umarni da ya saba da ranar da aka sanar da daina karbar tsaffin kudi tunda farko.
Sauran wadanda aka dakatar sun hada da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da babban bankin Nijeriya da kuma gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele.
- Sauya Takardun Kuɗi: Jam’iyyu Siyasa 13 A Nijeriya Sun Yi Barazanar Ƙaurace Wa Zaɓen 2023
- CBN Da ‘Yansanda Za Su Sa Kafar Wando Daya Da Masu Sayar Da Sabbin Kudi
Wannan na kunshe cikin wani kudiri da jam’iyyun siyasa biyar daga cikin 18 suka gabatar a gaban Mai shari’a Enenche, ya kuma bayar da umarnin shugabannin bankunan da masu sauya da tsaki kan lamarin kan ka da su saba da umarnin na kotun.
Umurnin ya ja kunnen shugabannin bankin da ma’aikatansu da ake zargin suna boye sabbin takardun kudi da nufin yin kasuwanci da su wanda hakan ya jawo wa ‘Yan Nijeriya shan bakar wahala.