Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta soke zaben kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Liman ta, kuma bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe biyar a mazabar Makera.
Idan ba a manta ba a ranar 30 ga Satumba, 2023 ne kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kaduna ta soke nasarar da Liman mai wakiltar mazabar Makera ya samu tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 42.
- Kotu Ta Daure Wani Dan Kasuwa Bisa Laifin Satar Kayan Kanti
- Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Inuwa
A bisa rashin amincewa da hukuncin kotun, dan takarar jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) suka garzaya kotun daukaka kara kan hukuncin da kotun farko ta yanke.
Sai dai kotun daukaka kara a hukuncin da mai shari’a O. O Adejumo, mai shari’a A. Oyetula, da mai shari’a P. A Obiora a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba, 2023, a Abuja, suka yanke, sun yi watsi da karar da shugaban majalisar da INEC suka yi, tare da bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe biyar maimakon 42 da kotun farko ta bayar.
A halin yanzu, APC na da kuri’u 17,470 yayin da PDP ke da kuri’u 17,088