Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Usman Tilde, ya yi murabus daga mukaminsa.
Tilde, wanda ya wallafa wannan batun a shafinsa na Facebook, ya ce, ya aike da wasikar bukatar neman yin murabus wa gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi domin neman damar amsa kiran wani da ke tsananin bukatar aikinsa.
Ya ce, “Fatana a ranar Alhamis da fita daga ofis, na aike da wasikar zuwa ga gwamnan Jihar Bauchi da ya ba ni dama na amsa kiran wani aboki da ke bukatar aikina.”
Ya kara da cewa, bukatarsa ta kai ga samun nasara domin a ranar Litinin 5 ga watan Disamba ya samu wasika daga wajen sakataren Gwamnatin jihar, inda ke shaida masa cewa gwamna ya amince da bukatarsa ta ajiye aiki a matsayin kwamishina, daga bisa gwamnan ya gode masa bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta sashin ilimi a jihar.
Kana, gwamnan ya masa fatan samun rayuwa mai inganci a nan gaba.
Usman Tilde ya ce, wa’adin zamansa a matsayin kwamishinan ilimi ya kare, ya nuna farin cikinsa bisa kammala aikin da ya yi cikin kwanciyar hankali da nasara tare da ganin taimakon Allah cikin lamura. Ya yi fatan Allah zai cigaba da taimakonsa a sabon aikin da zai fara a nan gaba.
Daga nan ya gode wa gwamnan Jihar Bala Muhammad da al’ummar jihar Bauchi bisa damar da suka ba shi na yin hidima a matsayin kwamishinan ilimi na tsawon sama da shekara uku.
Daga bisa ya kuma jinjina tare da gode wa ma’aikatan hukumar Ilimi ta jihar, ofisoshin shiyya, makarantu, Malamai, kungiyar iyayen dalibai, abokan jere, kungiyoy masu zaman kansu a bisa goyon baya da taimakon da suka ba shi.