Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya ayyana gobe Juma’a 21 ga watan Afirlu a matsayin ranar Sallah.
Hakan ya biyo bayan ganin jinjirin watan Shawwal na shekara ta 1444 bayan hijira a wurare da dama a fadin kasar nan.
- Buhari Ya Dakatar Da Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa
- Bunkasuwar Kasar Sin Mai Inganci Ta Ingiza Kwarewar Jama’arta
A cewar sarkin, kwamitin ganin wata na kasa ya tabbatar da rahoton ganin jinjirin watan.
Don haka ya yi kira ga Musulmi da su zauna lafiya da juna ba tare da la’akari da sabanin da ke tsakaninsu ba.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya shiryar da sabbin shugabanninmu ya kuma yi wa kasarmu albarka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp