Dakarun soji sun yu nasarar cafke wadanda suka kai hari cocin Owo da ke Jihar Ondo, wanda ya yi ajalin mutane da yawa tare da raunata da dama.
Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa sojoji tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kama wasu ‘yan ta’adda da suka kai hari coci a garin Owo a jihar Ondo.
- Dan Sanda Ya Mutu A Harin Da ISWAP Ta Kai Hanyar Maiduguri-Damaturu
- Tsohon Shugaban Hukumar Binciken Sararin Samaniya Ta Kasa NARSDA, Ya Rasu
Ya bayyana haka ne a safiyar ranar Talata a jawabinsa a taron manema labarai na babban hafsan hafsoshin tsaro tare da shugabannin kafafen yada labarai a hedikwatar tsaro (DHQ) da ke Abuja.
An kai wa cocin Katolika da ke Owo hari a ranar 5 ga watan Yuni, 2022, wanda ya yi sanadiyar mutuwar masu ibada da dama.
Ya ce sojoji sun kuma kashe ‘yan bindiga da dama da ke aika ta’addanci a kasar nan.
Irabor, a harin da jirgin kasan Kaduna da aka kai, ya ce sojoji na kokarin ganin an ceto fasinjojin da aka yi garkuwa da su kamar yadda shugaban kasar ya umarta.