Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Nijeriya da yammacin ranar Laraba zuwa Turai.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Tunde Rahman, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa zababben shugaban ya kai ziyarar aiki kuma yana shirin tattaunawa da masu zuba jari da sauran manyan abokan huldarsa domin daidaita shirin mika mulki tare da wasu manyan mukarrabansa.
- Nijeriya Da Birtaniya Sun Kulla Yarjejeniya Kare Hakkin Bakin Haure
- Kawu Sumaila Ya Gargadi Tinubu Kan Yi Wa Majalisa Katsa-Landan
Sanarwar dai ba ta bayyana ainihin inda nufa a nahiyar Turai ba amma ta bayyana cewa zai dawo nan ba da dadewa ba domin shirye-shiryen rantsar da shi a hukumance a matsayin shugaban kasar Nijeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayun 2023.