Babban kuma fitaccen ma’aikacin banki sannan wanda ya asassa tare da kafa Bankin ‘First City Monument Bank’ (FCMB), Chief Michael Olasubomi ‘Subomi’ Balogun, ya mutu yana da shekara 89 a duniya.
An labarto cewa ya rasu ne a wani asibitin a birnin Landan ta kasar Burtaniya da safiyar ranar Juma’a.
Chief Balogun shi ke rike da sarautar Otunba Tunwase na Ijebuland kuma shi ne Olori Omoba na Masarautar Ijebuland, kazalika na rike da sarautar Asiwaju Onigbabo Ile Ijebu (Shugaban kiristoci ‘yan asalin Ijebu).