Kafar sada zumunta ta WhatsApp ta samu matsala da sanyin safiyar ranar Talata, lamarin da ya sanya sama da mutane 12,000 suka wallafa cewar kafar tasu ta daina aiki.
Tsayawar WhatsApp ba iya Nijeriya ta tsaya ba, lamarin ya shafi kusan duka kasashen duniya da ke amfani da kafar ne.
- Da Dumi-Dumi: Kafar WhatsApp Ta Daina Aiki
- Buhari Ya Bai Wa Ministan Ruwa Wa’adin Wata 3 Don Kawo Karshen Ambaliyar Ruwa A Nijeriya
Tuni dai dubban mutane suka shiga sauran kafafen sada zumunta kamar su Facebook, Twitter, Instagram da sauransu suka dinga wallafa korafi kan tsayawar WhatsApp din.
Akalla mutane biliyan biyu ne ke amfani da kafar sadarwar ta WhatsApp a fadin duniya.
A shekarar da ta gabata irin wannan matsala ta samu kafar ta WhatsApp wadda mallakim kamfanin Meta ne.
Hakan ya janyowa kamfanin asarar maduden kudade masu tarin yawa.