‘Yan bindigar da yi awon gaba da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, sun saki sako mutane uku bayan sakin bidiyon da suka yi suna dukansu a daji.
Rahotanni sun bayyana an sako mace daya da maza biyu.
- Manoman Kano Sun Koma Noman Dawa Saboda Tsadar Taki
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Mahara 2 A Anambra, Sun Kwato Makamai
Da fari an sako mutane uku daga cikin fasinjojin da suka sace na harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, na hudun kuma sun sake shi kwanaki shida da suka shude.
Wadanda aka saki su ne Oluwatoyin Ojo, Hassan Lawan da Fasto Ayodeji Oyewumi, yayin da kuma Misis Gladys Brumen ta kubuta tun tuni.
Hassan shi ne mutumin da ya yi magana a bidiyon da ‘yan ta’addar suka saki a ranar Asabar, wanda ya yi kira ga gwamnatin manyan kasashen duniya da su kai musu dauki
A ranar Asabar da ta gabata ne, ‘yan bindigar suka daki wani bidiyo mai tsagin kusa minti 11, suna dukan fasinjojin don tumzura gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Hakazalika, ‘yan bindigar a cikin bidiyon sun barazanar yin garkuwa fa shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Sai dai fitar bidiyon ta bar baya da kura, mutane na ta tofa albarkacin bakinsu, game da yadda gwamnatin tarayya ta gaza kwato fasinjojin da aka sace sama da kwana 100.