Shaharariyyar mai zanen barkwanci na “Cartoon” ta kasar Amurka Ann Telnaes ta sanar da janye jikinta daga jaridar Washington Post a kwanakin baya, wurin da ta kwashe kusan shekaru 17 tana aiki bisa dalilin cewa, jaridar ta ki wallafa wani zanen da ta zana, wanda ya zargi dadin bakin da shugaban jaridar Jeff Bezos ya yi wa zababben shugaban kasar Donald Trump.
Telnaes ta ce, an ki yarda da zanenta ne kawai saboda ra’ayin dake ciki, kuma wannan ya kasance wata barazana ga ‘yancin yada labarai.
- Sanwo-Olu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 3.366 Na 2025
- Sukar Gwamnatin Tinubu: Haƙiƙanin Gaskiyar Kama Obi A Abuja
Ko sanannun mutane kamar Ann Telnaes ba su da ‘yancin fadin albarkacin bakinsu, to ina ga sauran jama’a? Baya ga haka, in mu duba halin da TikTok ke ciki a Amurka, wannan manhaja ta samar da wani dandali mai kyau ga jama’a da suke bayyana ra’ayoyinsu, amma gwamnatin Amurka tana neman kwace shi bisa hujjar tsaron kasar, kuma idan TikTok ya ki sayar da kansa ga Amurka, to, za ta haramta shi a kasar.
Shin ko da gaske ne Amurka tana kare ‘yancin fadin albarkacin baki da yada labarai? (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp