Kishi kumallon mata. Shafin TASKIRA shafi ne da yake zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, wadanda suka hadar da; Zamantakewar aure, Rayuwar yau da kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu. Sai dai kuma shafin yakan canja akalarsa wani lokacin wajen maida hankali ga karbar sakonnin masu karatu, musamman masu matsalolin da suke bukatar a tattaunawa a kai dan samun mafita da shawarwarin ma’abota shafin.
Tsokacinmu na yau wani babban al’amari ne wanda shafin ya ci karo da shi, wani labari ne me ta da hankalin mai hankali, wanda yake cike da ban mamaki da al’ajabi, wanda aka nemi a sakaya suna. Labarin dai shi ne: Wata mata ce bahaushiya, musulma, me tsananin kishin tsiya, wadda kishin nata ya wuce misali, kishi ne tamkar irin na masu tabin kwakwalwa. Wadda ke da kusanci da matar da har ila yau ita ce ta aiko mana da wannan sakon ta ce; ‘Matar ta yi ikirari a kan cewa; Da Mijinta ya yi mata kishiya gara ya dinga amfani da yaranta mata da Allah ya ba su guda biyar, matar ta ce; a duk ranar da yake da bukata ya gaya mata wacce ya ke bukata za ta kawo masa ita da kanta’. Wa’iyazubillah.. Ko ya za a kira hakan da shi? Wadanne hanyoyi ya kamata mata su bi domin tursasa zukatansu, da bawa kwakwalwarsu damar yin tunani me kyau ko dan gudun fadawa tarkon da-na-sani? Wannan ya sa shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu, ga kuma ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Zainab Abdullahi (Lailat) daga Jihar Katsina:
Hankalina ya matukar tashi bayan cin karo da nayi da wannan bakin labari, wanda kafin yanzu ban taba jin labarin kazanta ma fi muni wanda ya girgiza ni ba kamar shi. Wannan abun kunyar da suka aikata ya fi karfin a kira shi da kwamacala sai dai jagwalgwalin kwamacala. Saboda tsagwaron tsabagen hauka ki sadaukar da mutuncin yaranki ga mahaifinsu domin kada ya auro wata matar, shi kuma ya biye miki ku ka taka rawa da gangar da shaidan ya buga muku mai zaki ba tare da kun hasaso abin da zai faru a gaba ba. Kowace uwa kullum kokari take wurin ganin ta tsare mutunci da darajar yaranta mata da Allah ya bata, abin mamaki sai ga wata uwar ta sadaukar da wannan mutuncin na yaranta ga mahaifinsu saboda tsananin tabewar basira irin nata. Don haka wannan ba kishi bane dabbanci ne, kai ko dabba ma ban tunanin za ta aikata wannan shirmen. Kishi abu ne da zamani ko lokaci ne kadai za su iya fayyace muninsa ko kyawunsa, alkairinsa ko sharrinsa. To ga alamu wannan zamanin da muke ciki bala’i da sharrin dake cikin kishi, ya ninka alkairi da kyawunsa yawa sau ninkin ba ninkin. Yau sai ka ji an ce wata ta dabawa mijinta wuka, sai ka ji an ce wata ta watsawa kishiyarta ruwan zafi. Ga su nan babu adadi misalan, kullum da sabon salon haukan da wasu matan ke zuwa da shi wai duk da sunan kishi, Allah ya wadaran irin wannan kishin. Kuma idan har suka bari suka mutu ba tare da sun tuba ba, lalle sai Allah ya hukunta su akan wannan kazantar ta su. Ya kamata mu ji tsoron Allah mu kuma dinga tunawa da ziyarar da Manzon Allah ya kai a wuta kuma ya ga ma fi yawanci mata ne a cikinta, ya fada mana ne don mu hankalta, domin ya san irin wannan zamanin zai zo. Kishi ba hauka bane, mu yi kishi na hankali da sanin ya kamata, Allah ya ganar da mu.
Sunana Lubabatu Auta ingawa Daga Jihar Katsina:
A gaskiyar maganar akwai bukatar binciken kwa-kwalen wasu matan. Mace Mai cikakkiyar lafiya da ilimi bana tunanin za ta yi wannan maganar. Saboda gudun kishiya shi ne za ta ce ta yarda mijinta ya biya bukata da ‘ya’yansu, ai wannan ya tashi daga kishi ya koma tsantsar hauka. Maganar gaskiya ya kamata mata mu cire son zuciya mu ji tsoron Allah, mu koma hayyacinmu, sannan mu dage da neman Ilimin addini domin tabbas irin wannan kishin na wasu matan yanzu akwai tsantsar jahilci da rashin sanin ya kamata a cikinsa. Daga karshe ina ba mata shawara mu rage zafin kishi domin babu inda zai kai ku sai ga halaka. Ki kasance mai biyayya da kyautatawa mijinki da tsabta da kwalliya da gyaran jikinki, Hakan zai sa ko mijinki ya kara aure kima da darajarki suna nan a wurinsa kuma ba zai canza miki matsayi ba.
Sunana Haleema Khabir (Nana Haleema) daga Jihar Kano:
Na farko wannan jahilci za a kira shi ba batun kishi a cikin wannan sai dai a ace jahilci da rashin ilimin addini da kuma kekashewar zuciya, da kuma amfani da hudubar shaidan. Addu’a ita ce makamin mumini, a duk inda bawa yake matukar zai rike addu’a zance ya kare. Domin kuwa ‘power of du’a’ yana canja ‘destiny’, koda kaddara mara kyau za ta same ka indai za ka mika lamarin ga Allah hakika Allah zai canja maka ita ta koma ta alkhairi. Indai baka rike addu’a ba ba kuma su tsarkake zuciyar su babu wata hanya da tafi wannan, domin Manzon Allah (S.A.W) ya ce “In zuciya ta gyaru dukkan gangar jiki ta gyaru, in ta baci gangar jiki ta baci”. Matukar ba su kawar da shaidan sun mayar da shi baya ba sun mika lamarinsu ga Allah ba tabbas akwai tarin dana sani a gaba. ba shi da amfani domin babu abin da yake jawowa sai dana sani, an san kishi halak ne amma kishi mai tsafta shi ne halak ban da kishin hauka, domin duk kishin da zai ja mutum yayi kisa ko ya nemi a sabawa Allah ba halak bane ba. Kamar yadda na ce addu’a ita ce za ta zama maganin duk abin da yake zukatansu, sannan su rage sauraron zuga irin ta kawaye, a rage zama shiru in irin haka ya taso kamar miji ya sanar zai kara aure kar a dinga zama shiru a yawaita karatun alkur’ani. A mika lamari ga Allah duk abin da ya kaddara babu kishin da zai hana faruwarsa sai dai in daman bai kaddara faruwar sa ba. Zafin kishi karshe yana karewa ga matan da suke yin sane domin kin cuci kanki, ‘ya’yanki, rayuwarki, da komai naki ma, hatta lahirar ki kin lalata ta domin ko ba a fada ba kowa ya san tarin zunubin dake cikin abin da aka aikata.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:
Hmmm na rasa abin cewa.. A gaskiya wannan sai dai mu kira shi da tsantsan jahilci da toshewar basira. Haba Jama’a ai wannan abu yayi muni wallahi uwa fa Allah kasa mu yi kyakkyawan karshe dai, amma wannan tsagwaron toshewar basira har ina. To babban abin da ya kamata mata su rika shi ne; addu’a dan ita ce gaba da komai, sannan kuma a ringa kai zuciya nesa. A rintse ido ayi hakuri a gani ayi kamar ba a gani ba, kana in mace ta riski kanta a cikin jerin wadannan mata, to ta gujewa neman shawara wajen kawaye wani zubin sune kanwa uwar gamin kitsa komai. Ya kama mata dai a ringa sara ana duban bakin gatari kishi fa ba hauka ba ne. Ka da mu kai kanmu ga halaka dan Allah.
Sunana Shamsiyya Usman Manga daga Jiha Yobe:
Da farko dai wannan lamari ban ma san ta yadda zan fara ‘reply’ ba, amma bari na daure zuciyata na ce wani abu watakila dai sakon ya iya kaiwa wajen ita matar ko kuma masu zuciya irin tata. Wannan abin za mu iya kiran shi da jahilci kai tsaye, ko kuma mu ce mutuwar zuciya tabbas Annabin Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya yi gaskiya da ya ce (A cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru idan kuma ta baci dukkan jiki ya baci, wannan ita ce zuciya). Zuciya da mu ke gani mugun abu ce idan har za mu biye ta to ba abin da ba za ta sa mutum ya aikata ba. Mata mu ji tsoron Allah mu sani cewar su fa wadannan ‘ya’yan da muke gani amana ce a gare mu, kuma Allah sai ya tambaye mu akanta yadda mu ka tarbiyantar da yaranmu ranar gobe kiyama, ya ke ‘yaruwa ki sani cewa shi fa kishi ba hauka ba ne, sannan shi namiji idan fa ya yi niyyar aure kishinki na banza da wofi bai isa ya hana shi ya kara auren ba. Shawarata ga mata akan kishi shi ne don Allah su yi hakuri su dinga lallashin zuciyar su sannan su dinga tunawa da cewa shi karin auren ai ba haramun ba ne.
Sunana Musbahu Muhammad Goron Dutse Jihar Kano:
Tsabar hauka ne da Jahilci, ya kamata kafin su yi Auren su sani cewa Aure ibadah ne kuma duk Ibadah akwai yadda aka ce a yi ta. S annan su dinga tunani me zurfi kafin su furta wata kalma ko aikata wani abu wanda ya shafi kishi ko kishiya. Su daina batawa kansu lokaci tunda Allah ya halattawa maza yin Aure fiye da mace daya. Kuma su ma mazan suna son zama da mace fiye da daya.
Sunana Hajara Ahmad (Oum-Nass), Daga Garin Hadejia A Jihar Jigawa:
Za a kira hakan da Jahilci, wauta da kuma rashin sanin darajar kai, ba ga iya matar da ta yanke hukunci ba har ga mijin da ya dauki shawarar abar ji da saurara da kuma dauka. Sanya hankali tare da yin zurfin tunani kafin magana, Allah ya ba wa dan Adam hankali domin ya yi nazari kafin zartar da kowanne irin hukunci. Akwai bukatar yin shiru da dogon nazari, tausasa zuciya da bata hakuri akan dukkan rudadden Al’amarin da ya zo, wannan hanyar ita ce mafi kyau da dacewar da za ta samar da magana mai kyau a lokacin da aka furta. Wannan ba kishi za a kira shi ba, sai dai Hauka da Jahilci, ba mamaki Mutanen da suka aikata hakan su na da tabin hankali ko kuma rashin wadataccen ilmin Addini a tare dasu. NB; Babu wata Uwa cikakkiyar Uwa mai hankali da ilmin da za ta zabi wannan hanyar a matsayin mafita na gujewa zafin kishinta, Sannan masu tsananin zafin kishin k’in zama da kishiya ko na jikinsu ne ba su burin ya rabi abin da suke wa kishin bare kuma ‘ya’yan cikinsu, Allah ya tsare mu.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary Rano) Rano Jihar Kano:
Maganar gaskiya wannan jahici da hauka za a kira shi, sabida komai kishi mai hankali bai kamata tayi wannan aikin ba sabida ‘ya’yanta fa za ta yarda yayi zina da su wa iyazibillah. Hanyoyin da ya kamata su bi sun hada da aiki da ilmi, suna tuna cewa shi namiji ba wai an yo shi domin mace guda daya ba, suna duba gidajen aure a wannan zamanin mafiya yawa ba mace daya ce a gidan aure ba, sannan suna tuna cewa tunda har Allah ya ce namiji ya auri mace sama da 1 to ba yin kan namijin bane. Sannan wasu matan ma idan za su duba iyayensu mata za su ga su ma an yi musu kishiya. To shawarata anan ita ce; suna tuna cewa ita fa kishiya abokiyar zama ce, kuma Allah ne ya halasta ayi ta kamar yadda ta yarda Allah ya hakasta mata tayi aure. Sannan wallahi indai har za ki yi wa mijinki biyayya yadda addini ya tanada idanma da hali ki yi kari akan abin da ki ka san maigidanki yana da bukata ba kishiya ba koda zai auri matan duniya wallahi ba za ta taba ganin wani canji daga mijinta ba, kowacce da halinta za ta zauna.
Sunana Abba Gada Rano Unguwar Gada Rano LGA Jihar Kano:
Innalilahi wa’inna ilaihir Raj’un.. Gaskiya jahila ce ko in ce ba musulma bace dan wacce take da ilimin addini ko yaya yake ba za ta yi haka ba, wallahi farko ya kamata su sani cewa aure bautar Allah ne, kuma manzon Allah yayi auren nan sama da daya, dan haka sai ki shafa wa kanki ruwa indai kin bi tafarkin addinin musulunci, dan baki kai su daraja ba. Sannan mu mazan mu yi musa adalci hakan zai sa su cire kishi a ransu. Gaskiya masu irin wanan kishin ba shawara suke bukata ba ilimi suke bukata, makaranta ya kamata akai su su fahimci addini.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi (Dr.haibat):
A gaskiya mata ya kamata musan iri kishin da za mu yi, kada ya kai mu da halaka kada a biye wa son zuciya saboda zuciyar ba tada kashi sai dai tana da rami a cikinta har guda hudu. Dan Allah kada mu biye wa sharrin zuciya, wannan ayuwa ba tada tabbas, wannan muguwar rayuwa ce, ya kamata mu ke amfani da hankali da kuma lokaci. Kishi dole ne amma koda za ki yi ki yi abun da ba za ki do kina nadama ba, kiyi kishi irin na matan sahabbai, ki kalli haguki da damanki ba daya suke ba, ballantana miji wanda ba danki bane, Allah ya sa gobenmu ya fi farko mu kyau.
Sunana Usman Abdullahi (Abba Goma) daga Jihar Kano:
La’ilaha illallah…. Allah ya kawo mana sauki a cikin zukatan mu, wannan masifa tayi yawa, mata sun zamar da aure masifa Allah ya yi mana maganin wannan tashin hankalin. Wannan matar gaskiya ya kamata maza su san wani irin mace za su aure tun kafin a wayi gari da ire-iren wannan masifa. A gaskiya ya kamata malamai su sake dagewa da yi wa mata da maza wa’azi tun kafi aure, saboda wasu matan har yanzo Basu san me ake nufi da aure ba, Allah ya sa mu dace.