Kwamitin haɗin gwuiwa kan Lamuran zaɓe ya ba da shawarar a rage albashin ‘yan majalisa da mambobin gwamnati domin rage kashe kuɗi. Sun bayar da shawarar a rage albashin ‘yan majalisa da kashi 30%, sannan a rage albashin mambobin gwamnati da kashi 40%. An tattauna wannan shirin ne a wani zama na tattaunawa da aka gudanar ranar Litinin, wanda ya haɗa da mambobin ɓangaren Shari’a da jam’iyyun siyasa.
Baya ga rage albashi, jam’iyyun siyasa sun ba da shawarar cewa duk zabubbuka—na shugaban ƙasa, da majalisar dokoki, da gwamna, da majalisar dokokin jihohi—su kasance a rana guda domin rage kashe kuɗi. Haka kuma, sun bada shawarar a haɗa rijistar masu zaɓe da Lambar Shaidar Ƙasa (NIN) domin samar da tsaro mai kyau da kuma rage kashe kuɗi.
- An Kama ‘Yan Shi’a 97 Kan Kisan ‘Yansanda 2 Abuja
- Zaben Kananan Hukumomin Kano: ‘Yan Takara 400 Na Tururuwar Kamun Kafa A NNPP
Daga cikin shawarwari 35 da shugaban kwamitin IPAC harya gabatar, akwai kiraye-kirayen a sauya hanyar naɗa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), inda suka ba da shawarar cewa a tallata wannan matsayin maimakon a bar shi ga ɓangaren zartarwa.
Sanata Sharafadeen Alli, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan lamuran Zaɓe, ya tabbatar da cewa kwamitin zai nemi ƙarin shawarwari daga INEC da jama’a domin tabbatar da cewa zabubbuka masu zuwa sun gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba.