Rumfar kasar Sin a taron kasashen da suka kulla yarjejeniyar hana kwararar hamada ta MDD karo na 16 wato COP 16, ta gudanar da karamin taro a kwanan baya, mai taken“Fasahar kiyaye muhalli da makoma mai kyau”, inda kasar Sin ta yi musayar dabarun samun ci gaban hadin gwiwarta da sauran kasashe a bangaren hana yaduwar hamada. A hakika dai, har kullum Sin na bude kofarta ga sauran kasashe kan more dabarar hana kwararar hamada, don samar da gudummawarta ga kasashen da suka yi fama da wannan matsala.
Afirka nahiya ce da ta fi fama da kwararar hamada a duniya, hukumar kiyaye muhalli ta MDD ta ba da alkaluma cewa, filayen da yawansu ya kai kashi 45% na fadin nahiyar Afirka na fama da kwararar hamada a mabambantan matakai. Don kare kwararar hamada, kasashen Afirka na gudanar da jerin shirye-shirye, musamman ma shirin “babbar ganuwar itatuwa ta Afirka ”.
- Kasar Sin Ta Gudanar Da Muhimmin Taron Tattalin Arziki Don Tsara Ayyukan 2025
- Gwamnatin Tinubu Na Amfani Da Kuɗaɗen Tallafin Mai Don Ci Gaban Al’umma – Minista
Don tallafa wa kasashen Afirka a kokarinsu na hana kwararowar hamada, Kasar Sin ta sha gudanar da kwasa-kwasai din horar da kwararrun kasashen Afrika dangane da wannan shiri. A shekarar 2017 kuma, cibiyar nazarin yanayin halittu da yanayin kasa ta jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna da sakatariyar kungiyar babbar ganuwar itatuwa ta Afirka, ta yadda za su yi hadin gwiwa a bangaren sa ido kan tsarin muhallin halittu da amfani da albarkatun kasa cikin dorewa da horar da kwararru da samar da fasaha da sauransu, don kara karfin kasashen Afirka wajen yaki da kwararar hamada. A jihar Kano na Najeriya, cibiyar nazari ta hadin kan Sin da Afirka ta yi nazari kan matsalolin da ake fuskanta a wurin, ta kafa sabon salon shingen kare kwararar hamada da yankin gwaji na dasa itatuwan dake iya samar da arziki. Duba da iyakacin kokarin da Sin da kasashen Afirka suke yi, kason hamada a yankin Sahel ya ragu daga kashi 72.31% na shekarar 2000 zuwa kashi 69.23% na shekarar 2020.
Dabarar da Sin take samu da ma fasahar zamani da take da ita, ababen bukata ne ga Afirka tamkar ruwa a jallo wajen dakile kwarar hamada, an yi imanin cewa, kasashen Afirka za su kara karfinsu na daidaita muhallin halittu da samun bunkasuwa mai dorewa bisa fasahar zamani iri na kasar Sin, da aiwatar da manufofin Sin bisa yanayin da suke ciki. (Mai zane da rubutu: MINA)