A jiya Asabar ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bikin bude taron wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan Yarjejeniyar Ramsar, kan yankuna masu dausayi ko COP14 a takaice, wanda aka yi a birnin Wuhan, inda ya jaddada cewa, ya dace a kara samun fahimta, da fadada hadin-gwiwa, domin daukar matakan kiyaye yankuna masu dausayi a fadin duniya baki daya.
Shugaba Xi ya bayyana wasu ra’ayoyi uku, dangane da aikin kiyaye yankuna masu dausayi, al’amarin da ya tsara shirye-shirye ga kiyaye yankuna masu dausayi a duk duniya.
A wajen babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 da aka yi kwanan baya, an bayyana manufar farfado da al’ummomin kasar Sin daga dukkan fannoni, bisa zamanintar da kasar mai sigar musamman, kuma “kasancewar dan Adam, da muhallin halittu cikin jituwa” daya ne daga cikin wasu muhimman halaye biyar na zamanintar da kasar mai sigar musamman.
A cikin jawabin, shugaba Xi ya kuma gabatar da muhimman matakan da kasarsa za ta dauka a nan gaba, a fannin kiyaye yankuna masu dausayi, wadanda ke shaida cewa, kasar Sin za ta ci gaba da himmatuwa wajen shimfida zaman jituwa tsakanin dan Adam da muhallin halittu, da raya sha’anin kare yankuna masu dausayi ta hanyar da ta dace. (Murtala Zhang)