Assalamu alaikum iyaye barkanmu da war haka, sannunmu da arzikin sake haduwa a wannan fili namu mai farin mini RAINO DA TARBIYYA.
Yau filin zai yi duba ne a kan ROKO. Iyaye kan yi sakaci wurin kyale yaro ya tashi da dabi’ar ROKO har zuwa girmansa,hakan kan haifarwa wa yaro da mutuwar zuciya da rashin dogaro da kai.
- Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
- Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”
Roko wata dabi’a ce marar kyau da ke kashe zuciyar mai ita.Yana daga cikin tarbiyya na kwarai iyaye su sa ido su kula akan yara ,da zaran sun ga yaron da ya fara nuna alamar zai fara roko sai a yi saurin taka masa birki.
Wani yaron tun yana goye zaa ga in ya ga wani abu yana mika hannu ,irin wannan sai a buge hannun sa ko da an ba shi abin a hana shi.wasu iyaye kan ce ai yarone ba zaa dauki kowani iron matakiba ,a tunani da hankalinsa gani zai yi abu ne me kyau kuma yana kan daidai har wani lokaci in ya roka ba a ba shi ba ya yi ta kuka.
Wanda ya sbba da roko tun yana karami har zuwa girma irinsu ne in macece ta zama mai rokon samari har ta fada hannun macuci ya cutar da ita.
Idan namiji ne ya ki yin sana’a sai bibiyar masu kudi ko ‘yan siyasa saboda ya saba da sai ya roka ya samu.
Iyaye mu sa ni roko na haifar da daukar kayan wani ,yana zubar sa kima da mutuncin mai shi har da iyayensa,yana kuma kashe zuciya da dora rayuwa gabadaya akan tsammani mu kula matuka wurin hana yaranmu roko da daukar mummunan mataki a duk lokacin a muka ga sun yi ko aka bamu labari.
Allah ya sa mu gyara.