An fara yada addinin Musulunci zuwa birnin Beijing na kasar Sin a farkon karni na 10 daga yankin tsakiya da yammacin Asiya, da kuma tsakanin Indiya da Sin. Haka kuma, daga shekarar 996, aka fara gina masallacin Niujie dake birnin Beijing, wanda ya kasance daya daga cikin masallatan da aka fara ginawa a birnin.
Tsakanin shekarar 1644 zuwa shekarar 1910, addinin Musulunci ya yadu cikin sauri a birnin Beijing, ya zuwa shekarar 1948, adadin masallatan da aka gina a birnin Beijing ya kai guda 46, sa’an nan, ya zuwa shekarar 2021, adadin masallatan da aka gina a birnin Beijing ya karu zuwa guda 70.
- MASALLACIN NIUJIE
Titin Niujie, titi ne mai dogon tarihi dake nuna al’adun al’umma, yanzu an sabunta shi bayan gyaran da aka yi masa. Inda ya sha bamban da sauran titunan Beijing, sama da ’yan kabilar Hui dubu goma ne ke zaune a titin, kuma shi ne titi mafi girma da aka fi samun ’yan kaiblar Hui.
- Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Da NATO Ta Yi Mata
- Kasar Sin Ta Samar Da Motoci Masu Amfani Da Wutar Lantarki Miliyan 20
Yau wajen shekaru dubu daya ke nan musulman kasar Sin suka fara rayuwa a titin. Ginin da ya fi shahara a kan titin, shi ne Masallacin Niujie.
Masallacin Niujie, masallaci mafi girma da tsawon tarihi a Beijing. An yi masa gyara har sau biyar domin kara kawata shi, wannan ya shi zama masallaci mai kayatarwa. Fadin masallacin Niujie ya kai muraba’in mita 1500, ya kunshi wurin salla da dakin karatu. Kowace rana musulmai da dama ne ke zuwa domin yin Ibada, musamman ma a lokitan babba da karamar salla. Wasu musulmai daga sassan duniya ma na zuwa masallacin don yin salla, tare da musulman kasar Sin. Wuri mafi muhimmanci a masallacin shi ne kwaryar masallacin.
An gina shi ne a bangaren yammanci daga taswirar Makka watgo dakin Qa’aba. Musulmai 1000 ne ke salla a kwaryar masallacin mai fadin muraba’in mita 600. An zana hotunan al’adun Larabawa a ginshikan dake cikin dakin, an kuma kawata kofofi da tagogin da rubutun Larabci, ana iya ganin rubutun Larabci ta ko’ina. Ban da haka kuma, an jera litattafi da muhimman takardun addinin musulunci da dama a ciki, baya ga nuna al’adun tarihi, sun kuma shaida ci gaban addinin musulunci a kasar Sin.
- MASALLACIN DONGSI
Masallacin Dongsi yana yankin Dongcheng na birnin Beijing, wasu na cewa, a shekarar 1356 ne aka kafa masallacin, amma, wasu suna cewa, a shekarar 1447. Musulmai sama da 500 ne ke salla a babban zauren, kuma cikin dakin adana bayanai na masallacin, akwai Alkur’ani mai tsarki iri daban daban. Kuma, a halin yanzu, masallacin Dongsi ya zama ofishin kungiyar addinin Musulunci na birnin Beijing.
- MASALLACIN QIANMEN
An kafa Masallacin Qianmen a shekarar 1680, sa’an nan, an gyara shi a shekarar 1795. Salon ginin ya nuna yadda mutanen arewacin kasar Sin na zamanin daular Qing suke gina masallatai, kuma, an kiyaye wannan masallaci da kyau.
A da, akwai wani littafin Alkur’ani mai tsarki da wani mutumin zamanin da ya rubuta da hannu, da akwatin gargajiya da ake adana litattafan addinin Musulunci a masallacin.
Tsakanin shekarar 1636 zuwa shekarar 1949, akwai musulmai da yawa da suka gudanar da harkokin kasuwanci a wajen yankin Qianmen, shi ya sa, a lokacin, aka samu mutane da yawa da suke sallah a Masallacin Qianmen, inda adadinsu ya kai sama da 2500.
Fadin Masallacin Qianmen ya kai muraba’in mita 1800, sannan nan akwai wasu muhimman turaka guda shida, wadanda aka sassaka bayanai da harshen Larabci, baya ga wani dutsen da shi ma aka sassaka bayanai da harshen Larabci, wanda yake da tarihin sama da shekaru dari 6. Wadannan kayayyaki ne masu taraja! Shi ya sa, masana su kan kai ziyara wannan masallaci domin kara fahimtar tarihin addinin Musulunci a kasar Sin.
- MASALLACIN HUASHI
An fara gina masallacin Huashi a shekarar 1415, daga baya, an sha yiwa masallacin gyara tsakanin shekarar 1368 zuwa shekarar 1912. A halin yanzu, gaba daya, fadin masallacin ya kai kimanin muraba’in mita 2000, ciki har da dakuna iri-iri guda 81. Kuma, fadin babban zauren cikin masallacin Huashi ya kai muraba’in mita 500, inda musulmai da yawa suke salla a lokaci guda.
- MASALLACIN DOUDIAN
Masallacin Doudian yana yankin Fangshan na birnin Beijing, kuma, shi ne masallaci mafi girma dake birnin Beijing, inda mutane 1500 ke gudanar da ibadar sallah a lokaci guda. A zamanin baya kuma, akwai wani tsohon masallaci a garin Doudian, wanda aka gina a shekarar 1713. Sa’an nan, an fara gina sabon masallaci na garin Doudian a ranar 9 ga watan Agusta na shekarar 2011, an kuma kammala aikin ginin masallacin a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2017, kana, an fara amfani da shi a lokacin karamar salla.
Ko wane bangare na ginin Masallacin Doudian yana da ma’ana ta musamma, tsawon babban zauren ya kai mita 40, wadda ke nufin, Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya zama annabi yana da shekaru 40. Kuma, akwai gine-ginen ganin wata guda biyu dake bangaren kudu da arewacin masallacin, wadanda tsawonsu ya kai mita 63, wato, annabi Muhammad ya tafi gidan gaskiya a shekarunsa na 63. Haka kuma, an hada al’adun wurin a lokacin da aka gina Masallacin Doudian, kamar a cikin alamar Masallacin Doudian, an hada tambarin garin Doudian da wani irin furen lotus da ake samunsu musamman a yankin Fangshan.
Akwai ’yan kananan kabilu daban daban da suke zama a garin Doudian, kamar ’yan kabilar Hui da ’yan kabilar Man da sauransu, shi ya sa, baya ga masallacin da aka gina a garin Doudian, an kuma gina gidan renon yara na kabilar Hui, da gidan kula da tsoffofi na kabilar Hui. Kuma, yawan musulmai ‘yan kabilar Hui dake zaune a garin Doudian ya kai kashi 1 bisa 4 na dukkanin al’ummomin garin, adadin da ya kai sama da dubu 1. A halin yanzu kuma, gwamnatin wurin ta shigar da Masallacin Doudian cikin jerin wuraren fadakar da jama’a kan ra’ayin kishin kasa da kuma jerin wuraren yawon shakatawa mai daraja na kasar Sin.
- MASALLACIN ZHENGYUAN
An kafa Masallacin Zhengyuan tsakanin shekarar 1821 zuwa shekarar 1850, a wancan lokaci, Masallacin ba shi da girma, akwai babban zaure, da dakin Liman, da wurin walwala da sauranasu. Sa’an nan, a watan Yulin shekarar 1997, an gyara tare da fadada wannan Masallaci, yanzu, fadin da ya kai muraba’in mita dubu 1.
Masallacin Zhengyuan masallaci ne mai salon kasashen Larabawa, kuma, an hada wasu kayayyaki na salon gargajiyar Sin a yayin da ake gina wannan masallaci, kamar hasumiyar kofar shiga mai kyau da kuma bangon kariya mai hade da ice da dutse da aka saka a gaban babbar kofar shiga. Hakika, ana iya cewa, Masallacin ya hada al’adun Larabawa da na kasar Sin.
- MASALLACIN YONGSHOU
Masallacin Yongshou yana yankin Xicheng na birnin Beijing, an fara gina masallacin a shekarar 1605, sa’an nan, an yi masa gyara a shekarar 1624.
MARYAM YANG