Bayan gwamnatin kasar Sin ta fitar da daftarin tabbatar da karkon jarin waje na shekarar 2025 a ranar 19 ga wata, masana sun ce, wannan daftari ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa bude kofa ga waje, da kuma fatan kasar Sin na yin hadin gwiwa da kamfanoni masu jarin waje domin cimma moriyar juna.
Cikin ’yan shekarun nan, kamfanoni masu jarin waje sun gane wa idanunsu manufar bude kofa ga waje ta kasar Sin, inda suka ba da gudummawa tare da cimma moriya. Kasar Sin tana dukufa wajen neman zamanantar da kanta ta hanyar inganta bunkasuwar kasar yadda ya kamata, tana kuma karfafa bude kofa ga waje. Daftarin da gwamnatin kasar ta fidda, za ta ba da gudummawa ga Sin wajen neman zamanantarwa, har ma da samar da damammaki ga kamfanoni masu jarin waje a fannin habaka kasuwanni da neman ci gaba, yayin da kuma zai taimaka musu wajen tunkarar kalubaloli iri-iri, ta yadda za su sami ci gaba cikin hadin gwiwa.
- Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
- Dangote Ya Koma Matsayi Na 86 A Jadawalin Masu Arziƙin Duniya
Cikin daftarin, an habaka hanyoyin zuba jari a fannoni daban daban, domin tabbatar da bunkasuwar kamfanoni masu jarin waje a kasar Sin. Ban da haka kuma, an samar da sauki ga kamfanoni masu jarin waje wajen gudanar da ayyukansu a kasar Sin, lamarin da ya taimaka musu a halin yanzu, har ma zai ba da gudummawa ga bunkasuwarsu a nan gaba. Rahoton da kungiyar ’yan kasuwan kasar Amurka dake nan kasar Sin, wato AmCham China ta fidda, ya nuna cewa, a bana, kamfanonin dake shafar harkokin saye da sayarwa kimanin kaso 70 bisa dari, za su zuba karin jari a kasar Sin.
Haka kuma, ana bukatar aiwatar da dukkanin matakan da aka ambata cikin daftarin kafin karshen shekarar 2025. Wannan wata kyakkyawar alama ce da kasar Sin ta samar wa kamfanoni masu jarin waje. An yi imani cewa, sakamakon jerin matakan da kasar Sin ta fidda domin tabbatar da karkon jarin waje, zai tabbatar da ganin kamfanoni masu jarin waje sun hadu da damammaki da dama a kasar Sin, tare da gano karin damammakin inganta kasuwanninsu a kasar. (Mai Fassara: Maryam Yang)