Shugaban hukumar ƙidayar Jama’a ta ƙasa (NPC), Nasir Kwarra, ya bayyana cewa an shirya gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje a shekarar 2025. Wannan sanarwa ta biyo bayan shekaru kusan 18 tun bayan ƙidayar ƙarshe da aka gudanar a 2006.
Kwarra ya bayyana hakan ne yayin taron tunawa da babban taron ICPD na Nairobi da aka gudanar a Abuja. Ya ce, “Jinkirin gudanar da ƙidayar ya zama babban ƙalubale, domin babu sahihin bayanai don ingantacciyar shawara.” Ya kuma ƙara da cewa gwamnati ta ƙudiri aniyar kammala aikin ƙidayar a shekarar gaba.
- Mai Da JamaA A Gaban Komai, Jigon Tsarin Raya Birnin Fuzhou
- Masana Afirka Sun Yabawa Halartar Shugaban Sin Xi Jinping Taron Kolin G20
Kwarra ya bayyana cewa rashin ƙidayar ya haifar da matsaloli wajen rarraba albarkatu da yanke shawarar da ta dace. Ya ce wannan matsala ta fi shafar yankunan karkara da kuma matasa, musamman mata da yara.
“Rashin bayanan da suka dace na hana ci gaba wajen kare hakkin lafiyar jima’i da samar da adalci ga jama’a,”
in ji shi.
A cewar hukumar, kidayar 2025 za ta bayar da ingantattun bayanai don tsara manufofi masu amfani da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.