Yayin da ‘yan ta’addan da ke addabar Babban Birnin Tarayya da jihohin Kaduna, Nasarawa da Neja ke kara karfi, rahotanni sun cewa ‘yan bindigar sun yi sansani a dajin Kajuru da ke yankin Kudancin Kaduna a Jihar ta Kaduna.
Majiyar tsaro ta bayyana cewa dajin da sojoji ke amfani da shi wajen horar da ma’aikatansu, an yi watsi da su, wanda hakan ya sa ya zama mafakar ‘yan ta’addan.
- Gwamnatin Zamfara Zata Raba Dabbobi Kyauta Ga Mata
- Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Sa ido Kan Tsaro A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
Kamar yadda PUNCH ta ruwaito, wata majiya ta ce “Yanzu haka masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifukan da ke ta’addanci a Babban Birnin Tarayya sun yi sansani a dajin Kajuru. Kajuru shalkwatar Karamar Hukumar Kajuru ce ta Jihar Kaduna. Dajin ya zama mafakar ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.
“Hakika, sojoji sun kashe tare da kama dimbin wadannan ’yan ta’adda a yankin a baya. Amma duk da yadda ake kama su, sai su koma wancan dajin tun da sojoji sun yi watsi da sansaninsu a garin.”
Majiyar ta kara da cewa, “Kisan gilla da yawa ya tilasta wa sojoji kafa sansanin wucin gadi a can, inda suke tsara dabarun fatattakar ’yan ta’addan kuma a zahiri abin ya yi wa jama’a kyau. Amma tun bayan tafiyarsu babu zaman lafiya a yankin, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi sun mamaye yankin.
Hakan na faruwa ne yayin da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya da ke aiki tare da rundunar ‘yansanda ta kasa (NPF), ta kame hanyoyin sadarwar ‘yan bindigar, inda ta bai wa ‘yansanda damar sanya ido kan hirarsu da motsinsu.
“Har ila yau, ’yansanda sun san inda ’yan fashin suke, yadda suke sadarwa, da kuma yadda suke yawo. Suna amfani da wayoyin wadanda suka sace. Suna binne wayoyin a cikin kasa kuma suna yin nisa daga wurin, sannan su dawo don tono wayar kuma suna yin waya a duk lokacin da suke son yin magana da dangin wadanda suka sace don neman kudin fansa.
“Kwana biyu kacal da kaddamar da runduna ta musamman a Abuja da IG, IRT ta kama wasu ‘yan bindiga biyu da wasu da ake zargi da yin garkuwa da mutane su hudu, wadanda ke addabar Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma al’ummomin da ke makwabtaka da su. “Har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyuka.” In ji majiyar.
A ranar Alhamis ta makon jiya, masu garkuwa da mutane sun kai farmaki a Kurudu da ke Abuja, a wani rukunin gidan sojoji inda suka yi awon gaba da wasu mutum uku da suka hada da matar aure da kuma surukin wani lauya, Cyril Adikwu.
Wani mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da aka yi garkuwa da mutane a gidan.
Ya ce, “Masu garkuwa da mutane sun kai hari a yankin da misalin karfe 9 na daren. Muna tsammanin mutum biyu ne kawai aka sace, amma daga baya hukumomin kula da gidaje sun tabbatar da cewa mutanen da aka sace su uku ne. Wadanda abin ya shafa dai matar lauya ce da surukinsa, da kuma wani mutum daya, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba. Harin ya ban tsoro saboda muna jin cewa muna cikin aminci a nan.
“Kamar yadda kuke gani, sojoji su zo nan daga shalkwatarsu. Sun kasance a nan tun lokacin da labarin ya bayyana, kuma sun toshe duk wata hanyar shiga gidan suna bincike a ko’ina. Ba wanda zai iya shiga sai in kai mazaunin gidan ne, kuma za a duba ka sosai.”
Wani mazaunin garin, Austine John, wanda ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa Adikwu ya yi nasarar tserewa. Lamarin ya fara ne da misalin karfe 10 na dare a lokacin da nan muka fara jin karar harbe-harbe, muka gane cewa akwai matsala. Na fita da sauri don ganin ko an kulle gate dina.
“Sai muka ji karar harbe-harbe a gidan Barista, daga nan ne muka sanar da mahukuntan gidan, inda nan take suka fara aiki. Cikin kankanin lokaci sojoji suka zagaya su ma suka fara harbe-harbe, amma kafin su zo, masu garkuwa da mutanen sun tafi da matar da kuma surukin Barista.
An cafke gawurtaccen mai garkuwa da mutane
Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta mika wani mutum da ta yi ikirarin cewa shi ne mai garkuwa da mutane a Abuja, Phillip Chinaza ga rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ce an kama Chinaza ne a Kaduna ranar Alhamis ta makon jiya lokacin da suke tserewa da wani mutum mai suna Segun Akinyemi daga Abuja zuwa Jihar Kano.
Hassan ya ce, “Jami’an, sun tare wata mota kirar Toyota Hilud mai launin toka mai lamba Abuja RBC 90 DC, dauke da fasinjoji hudu ciki har da direban, wadanda ake zargin motar ce ta kai masu garkuwa da mutanen.
“Da aka gane akwai matsala da kuma kokarin tserewa da suka yi, sai daya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya harbi ‘yansandan, kuma suka mayar da martani.
A sakamakon fafatawar da aka yi da bindiga, an kubutar da wanda aka sace, Segun Akinyemi da ke zaune a gida mai lamba 10, Flat 2, FCDA Kuarters, Area 3, Garki, Abuja, daya daga cikin masu garkuwa da mutanen kuma, mai suna Chinaza Philip na Life Camp, mai shekaru 28. Abuja, shi ma an kama shi.”
Sojojin Sama sun hallaka gawurtaccen dan fashin daji
Rundunar sojin saman Nijeriya ta yi karin haske kan yadda ta ce dakarunta suka kashe wani kasurgumin dan bindiga mai suna Janari, da mabiyansa da dama a wani sumame da suka kai karkarshin rundunar tabbatar da tsaro ta Operation WHIRL.
Rundunar ta bayyana cewa ta yi nasarar kawar da dan bindigan ne yayin da yake tattara mukarrabansa da niyyar kai hari a Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna.
Kakakin Rundunar, Air Bice Marshal Edward Gabkwet ya shaida wa BBC cewa rundunar ta sami nasarar ne bayan ta dauki lokaci tana dakon gungun ‘yan bindigar kafin su yi dace su yi arangama da su a yankin Gadar Katako da ke Karamar Hukumar Igabi.
‘Lamarin ya auku ne a ranar 18 ga watan Janairu, amma sai bayan ‘yan kwanaki muka sami tabbacin cewa an kashe wannan dan bindiga da mabiyansa. Shi wannan mutumin Janari mun sami labarin cewa yana da hannu cikin harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna’, kuma muna da tabbacin cewa yana da hannu a cikin hare-haren da ake kaiwa a hanyar Abuja zuwa Kaduna,’ in ji shi.