Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala daukar dan wasan gaba na RB Leipzig a kan kudi Yuro miliyan 60.
Nkunku ya koma Chelsea ne tun bara amma da yarjejeniyar cewar ba zai je koma kungiyar ta Ingila ba sai karshen kakar bana.
- Yadda ‘Yan Daba Suka Addabi Wasu Yankuna A Kano -Dan Majalisa
- Abubakar Y. Sulaiman Ya Sake Zama Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi
Likitoci sun auna lafiyarsa a Landan kuma ya saka hannu a kan yarjejeniyar shekaru 5.
Talla
Nkunku zai taimaka sosai wajen ci gaban kungiyar bayan ta kasa tabuka abin a zo a gani a kakar wasannin da ta gabata.
Shugaban Chelsea Todd Boehly yana Kokarin kyautata kungiyar ta Chelsea tun bayan sayen da ya yi mata a hannun Roman Abromavic.
Talla