A karshe dai, Nijeriya ta cire tallafin man fetur yayin da kamfanin NNPCL da safiyar Laraba ya sauya farashin famfunan man fetur dinsa zuwa Naira 537 kan kowace lita a Abuja.
Binciken LEADERSHIP ya nuna irin wannan yanayin a jihar Legas inda a yanzu kamfanin na NNPC ke sayar da man fetur a kan Naira 488 a kan kowace lita a gidan mansa da ke Old Ota Road, Abule-Egba, Legas yayin da na jihar Fatakwal kuma ake sayarwa akan Naira 511 kan kowace lita.
A jihar Filato farashin lita ya kai naira 537 a gidajen man NNPC.
Hakan sauran Jihohi baki daya, duk kamfanin ya Sauya farashi a gidajen man.
Wannan sauyi da kamfanin mai na kasa ya yi karin haske da bada tabbaci game da cire tallafin mai da ake cece-kuce akai.
Gwamnatin ta shaida cewa, tana kashe kusan dala biliyan 10 a duk shekara wajen bayar da tallafin man fetur din.