Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya shiga hannu, inda ta tsare shi.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da kama Yahaya Bello ga manema labarai a ranar Talata.
- Yahaya Bello Ya Samu Beli Bayan Cika Sharudan Kotu
- EFCC, ICPC Sun Kwato Naira Biliyan 277.69 Da Dala Miliyan 106 A Shekara Guda
Ya ce babban jami’in tsaro na hukumar ne ya kama Yahaya Bello.
A cewarsa, “Gaskiya mun samu nasarar kama shi, yana a hannunmu. Jami’an hukumar ne suka kama shi.”
A baya dai, LEADERSHIP ta ruwaito rahoto cewa Yahaya Bello ya je hedikwatar EFCC ne a safiyar ranar Talata tare da lauyoyinsa domin amsa tuhumar da ake masa na karkatar da kudade ba bisa ka’ida ba, wanda a bayan watanni ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa.
An bayyana cewa tsohon gwamnan ya je ofishin EFCC ne da lauyoyinsa ba tare da magajinsa ba, Gwamna Usman Ododo na Jihar Kogi, wanda ya biyo shi ofishin EFCC makonnin da suka gabata.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa wata tawagar masu bincike sun tsare Yahaya Bello a hedikwatar hukumar EFCC da ke gundumar Jabi a Abuja.
Idan dai za a iya tunawa a ranar 18 ga watan Afrilun 2024 ne hukumar ta ayyana tsohon gwamnan a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo tare da bayyana takardar sammacin kama shi kan zargin da ake masa na karkatar da kudade na naira biliyan 80.2.
A zaman karshe na shari’ar da aka yi masa a kotu na ranar 14 ga watan Nuwamba, EFCC ta bukaci a dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba a sabuwar shari’ar da ta shigar a kan Yahaya Bello, inda ta ce har yanzu kwanaki 30 za ta ci gaba da neman sammacin da aka yi a baya.
Sai dai hukumar EFCC ta amince da bayar da belin wadanda ake tuhumar Yahaya Bello da Umar Oricha, da Abdulsalami Hudu, inda ta kuma bukaci kotu ta kara wa wanda ake tuhuma na farko wato Yahaya Bello wa’adi domin gurfana a gaban kotu. Mai yiwuwa a gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu.