Bayanai da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar a ranar 28 ga watan Agusta sun nuna cewa, masana’antun sarrafa manhajar cikin kwamfuta ko software da fasahar sadarwa na kasar Sin sun ci gaba da samun daidato daga watan Janairu zuwa Yuli, yayin da kudin shiga na kasuwancin software ya kai yuan biliyan 6,457, wanda ya karu da kashi 13.6 cikin dari idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci na bara.
Sannan jimillar ribar da masana’antar kera software ta karu ta kai yuan biliyan 737.4, wanda ya karu da kashi 13.4 cikin dari idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci na bara.
A cikin kayayyaki masu amfani da software, kayayyakin masana’antu masu amfani da sofware sun yi fice, wanda ke nuna ci gaban harkokin fasahar zamani da masana’antu zuwa wani matsayi. (Yahaya)