Gwamnatin tarayya ta amince da wata sabuwar manufar bunkasa Ilimi ta hanyar fara koyarwa da harshen gado a firamare daga aji 1 zuwa 6.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta a fadar shugaban kasa.
A cewarsa, harshen gida za a yi amfani da shi ne kawai a shekaru shida na farko na ilimi yayin da za a hada shi da harshen Ingilishi a matakin kananan makarantun sakandare.
Adamu ya ce duk da cewa manufar ta fara aiki a hukumance, amma za a aiwatar da ita sosai idan gwamnati ta samar da kayan koyarwa da kwararrun malamai.
Ya ce harshen da za a yi amfani da shi a kowace makaranta shi ne yaran da yafi rinjaye ga mazauna yankin da makarantar take.