Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing ya bayyana a gun taron kolin dandalin siyasa na MDD game da batun ci gaba mai dorewa kan manufar raya ruwa mai dorewa da aka gudanar a jiya Talata, cewar akwai rashin hankali a nacewar gwamnatin Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliya na Fukushima sama da tan miliyan 1.3 cikin teku.
Dai Bing ya bayyana cewa, teku wani muhimmin bangare ne na tsarin ruwa na duniya, kuma kare muhallin teku wani nauyi ne da ya rataya a wuyan daukacin bil’adama. Wani abin da ke daure kai shi ne yadda gwamnatin kasar Japan ta kuduri aniyar zubar da sama da tan miliyan 1.3 na dagwalon ruwan nukiliya na Fukushima a cikin tekun ba tare da la’akari da damuwar kasashen duniya da ’yan adawar kasashen gabar tekun Pasifik da tsibirin ba. Matakin da zai yi matukar barazana ga muhallin teku da muhallin halittu na duniya, da rayuka da lafiyar mutane a dukkan kasashe, kuma rashin hankali ne.
Ya kamata kasashen duniya su dauki wannan batu da muhimmanci, su kuma bukaci kasar Japan da ta fuskanci halaltacciyar damuwar da bangarori daban daban, da dakatar da shirin zubar da dagwalon ruwan nukiliya a cikin teku, kana da tinkarar gurbataccen ruwa na nukiliya yadda ya kamata ta hanyar kimiyya, aminci kuma ba tare da rufa-rufa ba, da kuma yarda da tsauraran kulawa daga kasashen duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)