Darajar Naira ta sake faduwa a kasuwannin musayar kudaden ketare a Nijeriya, bayan da aka canjin Dalar Amurka guda kan Naira 803 a karshen mako.
Matakin dai na zuwa ne dai-dai lokacin da hauhawar farashin kayan masarufi ke kara ta’azzara.
- Lauyoyi 60 Sun Yi Karar DSS Kan Kin Sakin Emefiele
- Cire Tallafin Mai: Za A Fara Bai Wa Talakawa Dubu 8 Duk Wata
Alkaluma sun nuna yadda farashin dalar ya kai 803.9 a hannun hukuma yayin da a kasuwannin bayan fage farashin ya kai Naira 822 a ranakun karshen mako matakin da ke zuwa a dai-dai lokacin tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da tsananta a sassan kasar nan.
Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta fitar a ranar Litinin, ta sanar da kai wa kololuwa a hauhawar farashin kayan masarufi zuwa kashi 22.79 a watan Yuni karin 0.38 idan an kwatanta da hauhawar farashin da aka gani a watan Mayu.
Hauhawar farashin na Dala kai tsaye na shafar cinikayya a sassan Nijeriya, inda NBS ke bayyana cewa kayayyakin abinci su ne kan gaba wajen hauhawa wanda zuwa yanzu alkaluma ke nuna cewa karuwar farashin kayayyakin a jimlace ya karu da kashi 4.19 daga 2022 zuwa yanzu bayan da a shekarar da ta gabata hauhawar ta kai kashi 18.60.
Duk da yunkurin CBN na samar da farashin bai-daya a kokarin daidaita kasuwar musayar har yanzu ana ci gaba da ganin tashin farashin dalar kan mabanbantan farashi a kasuwannin gwamnati da na bayan fage, inda mako bayan mako farashin ke ci gaba tashi ba kakkautawa.
Hakan ya sanya talakawa shiga kokawa kan halin da suka tsinci kan su musamman game da tsadar kayan masarufi.