Rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA dake aiki a yankin gabashin kasar, ta gudanar da matakan soji a kusa da tsibirin Taiwan, inda ta harba wasu sabbin samfuran makaman roka masu rai zuwa sararin samaniya.
Da misalin karfe 1 na ranar jiya Alhamis ne rundunar ta gudanar da matakan, ta kuma yi nasarar sarrafa makaman rokar bisa tsarin aikin su.
Da yammacin ranar kuma, rundunar sojojin dake sarrafa rokoki, ta harba nau’o’in makamai masu linzami, cikin sassan gabashin teku, daura da gabashin tsibirin na Taiwan. Dukkanin makaman sun kai ga wuraren da aka tsara harba su cikin nasara.
Babban jami’in rundunar Liu Dongkun, ya ce dakarun za su cika aikin su da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai mulkin kasar, da kuma al’ummar Sinawa suka dora musu, na kare ikon mulkin kai da tsaron iyakokin kasar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp