A tsarin dimokuradiyya, wanda shi ne tsarin shugabancin da ya fi dacewa da karbuwa a wajen jama’a.
‘Yan siyasa suna yi wa masu zabe alkawuran da za su yi idan sun sami nasara.
- Abubuwan Kula Ga Masu Cutar Siga
- Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Tsige Shugaban NIRSAL, Aliyu Abdulhameed Kan Zargin Almundahanar Kudade
A bisa yarjejeniyar tsarin, masu zabe suna yin la’akari da abubuwan da suka amfana ko suka samu a lokacin da wa’adin ‘yan siyasa ya zo karshe.
Abu ne sananne ga ‘yan siyasa a lokacin da suka rike abin magana idan sun hau dandalin siyasa suna alkawuran samar da ingantaccen ruwan sha da gina hanyoyi da makarantu da inganta noma. Wadannan su ne alkawuran da ake yi wa talakawa, masu kudi da marasa kudi ko masu ilimi da marasa ilimi da duk dai wanda ake jagoranta.
A cewar Marigayi Malam Aminu Kano, masu rinjaye amma suka yi shiru ba sa iya magana, wato yawansu ba shi da amfani. Muddin suka kasance a tare da ‘yan siyasa, zai ba su damar samun nasarar zabe. Talakawa fa na son Shugaban kasa Muhammadu Buhari sosai da sosai.
A shekarar 2019, Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa zai fitar da mutum miliyan 100 daga kangin talauci kafin shekara ta 20230. Hakan na nuna cewa dole za a fitar da mutum miliyan 10 cikin talauci a shekarar 2020. Yanzu dai kasa da makonni 26 suka rage wa Buhari a mulki, wanda ake zaton dai wannan buri zai wuya a cimma shi. Abubuwa da dama sun taikama wajen kasa cimma wannan burin da aka tsara, wadanda suka hada da shiga kuncin rayuwa na matsin tatalin arziki da aka yi har karo biyu mabambanta, annoba da rashin tsaro da cin hanci rashawa da ciko da ake wa kasafin kudi da satar mai da rashin tsare-tsare yadda suka dace da sauransu.
Turawa na cewa daukar abu baibai ga tsarin gwamnatin da ake zato zai iya ba ka daidai tsarin da ake bukata. A watan Nuwamba shekarar 2022, wani rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bitar ya nuna cewa kasar ta sanya mutum miliyan 5 cikin matsanancin talauci a duk shekara na tsawon shekara 6 a maimakon a fitar da su cikin talauci. A yanzu akwai mutum miliyan 133 da suke cikin tsananin talauci da kuncin rayuwa a Nijeriya, wanda ya kai kashi 62.9% na yawan ‘yan Najeriya kenan. A shekarar 2016, mutum miliyan 103 ne suke zaune cikin talauci kimanin kashi 53.7 na ya wan ‘yan Nijeriya kenan.
Hukumar NBS ta yi kira da a dauki matakin gaggawa don kare mutane da shiga cikin kuncin rayuwa da kuma a kare su daga talauci.
Alamu na nuna cewa, mutum zai yi mamaki idan mutane sun zabi wannan gwamnati. Ba mamaki mutane ba su gane kurakuran da suka tafka ba, sun kasa daukan darasi daga kuskurensu baya wanda suka kasa yin canjin da ya kamace su. Haka kuma a matsayin mutum akwai lokutan da za mu tsaya mu rika bibiyan da aka yi ba daidai ba da yadda abubuwan suka faru.
Wasu suna kokarin bayanin dalilan da suka sanya gwamnatin Buhari ta kasa fitar da mutum miliyan 100 daga talauci, kamar yadda na gabatar a baya, amma dole ne mu fahimci ta yaya aka auna wannan talaucin. Rashin fahimtar yanayin zai kara fada wa wani matsalar da ta fi wanda ake zato.
A rahoton talauci da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar a shekarar 2022, wannan hukumar ta yi amfani da tsarin nan ne karbabbe na auna talauci da ake takaita shi da MPI a Turance. Wannan tsarin ba yana amfani da karancin kudi ba ne kadai kamar samun kasa da dala 1.9 a rana. Ya kara da rashin iya kula da lafiya da samun ingantaccen ilimi da rayuwa mai kyau da mutum yake yi. Safiyo din ya duba yadda mutane ba sa iya cin abinci mai kyau da biyan kudin makaranta da man girki da ruwan sha da wutar lantarki da maganar haya da abubuwan da ake amfani da su na bukatuwar yau da kullum a gida kamar su radiyo da wayoyi da kekuna da sauransu.
Cikakken bayanin wadannan abubuwan su ne batun abinci da wadataccen ruwa mai tsafta da rashin aikin yi da matsalar tsaro da ba ta lokacin karatu da yawan haihuwa wadanda suke kara talaucin. Wannan shi ne ta’arifin tsananin talauci a wajen Turawa.
Jihohin da ake da tsananin talauci da suka hada da Kano da take da mutum miliyan 10.5 da suke cikin talauci daga cikin yawan jama’an da suke jihar na milyan 14.7. Jihar Kaduna akwai matalauta miliyan 8 daga cikin mutum miliyan 9.6 da suke cikin jihar. Sauran su ne Jihar Katsina da ake da kusan mutum miliyan 7, a yayin da Jihar Sakwato da Jigawa da Bauchi suke da kusan mutum miliya shida-shida da suke cikin talauci. Daga cikin mutum miliyan 133 na matalauta, miliyan 86 suna zaune ne a yankin Arewa, yayin da miliyan 47 suke zaune a yankin Kudu. Hakan yana nufin kusan kashi 65 cikin 100 na matalautan da suke Nijeriya suna Arewa. Duk da karancin kudi, mutane ba su da isassun abubuwan da suke bukata na gudanar da rayuwarsu da suka hada da samun ilimi da lafiya da gidaje. A sakamakon haka, ya sanya aka sami kashi 84 cikin 100 na yara da suke kasa da shekaru 5 suke matalauta saboda rashin samun abun da kowani yaro ya kamata ya samu don dorewar rayuwarsa.
Kamar yadda muka sani shi talauci ba wai kawai zuwa yake ba, mutane suke kirkirarsa, inda mu a nan Nijeriya rashin shugabanci mai kyau ne ya kawo mana talauci. An riga an gina, har baya-bayan nan, mukan cutar da kanmu da na iyalanmu da sauran ‘yan’uwanmu. A duk lokacin da mutane suka yi kokarin samar da abu nasu masu zaman kansu, dukkanin abubuwan nan za su iya sauyawa. Wadanda kuma suke kan madafun iko sun yi babakere sun hana talakawa, suna tutiya da mallakarsu ne sun kuma hana su yin aiki da guminsu don su mallaki abun da suka mallaka.
A tsarin Nijeriya, mun ara wasu tsare-tsare ba tare da mun fahimce su ba, muna ta tunanin samun gaibu. Talauci kamar yadda muka sani an kirkire shi ne a kanmu. Ba mu da kwarewar da za mu iya amfanar da kanmu. Yadda ake samar da abinci da sha’anin lafiya da samar gidaje da tsaro gaba daya za mu iya cewa akwai rashin adalci a lamarin. Talauci ya zama wasu abun da suke amfani da shi don biyan bukatunsu a matsayin makaminsu.
A cewar Buhari game da nadin mai ba shi shawara a kan tattalin arziki, kashi 2.5% na kasar noma a Nijeriya aka noma a farkon shekara. Har yanzu ya kasa taimakawa wajen noman. Kwanan nan da kanshi yake cewa dokarsa ta rufe iyakoki ta sanya mutane sun koma gona sakamakon matsi na yunwa.
Wadanda suke son magance talauci sukan dauki kowani irin aiki domin kawar da talaucin. Za su iya aikin da suka san ba shi da kyau zai iya cutar da wasu ko muhalli tun da dai suna neman mafita ne.
Yankin Arewa da yake da akwai matalauta kusan kashi 65%, akwai filin noma, amma mutanen yankin na da karanci masu zuba jari. Kwanan nan Sanata Ndume ya yi kira ga majalisar dattawa ta gudanar da bincike kan bashin Naira biliyan 500 da bankin raya Nijeriya ya rarraba, wanda aka gudanar da rashin adalci a cikin lamarin. Kashi 11% aka rarraba a yankin Arewa, yayin da kashi 1% aka kai wa yankin Arewa maso Gabas. Legas ita kadai ta sami kashi 47%. Wani tsarin shi ne, sake fasalin naira wanda ya sanya abubuwa suka yi tsada ya kuma kara talauci a tsakanin al’umma.
Rage talauci a Nijeriya dole sai an yi abubuwa masu kyau sosai da suka hada da tsaron abinci wanda ya kai samun ingantaccen abinci da lafiya da samun ingantattun makarantu da rage ayyukan ta’addanci da rashin tsaro da ayyuka masu kyawun gaske. Mun san da cewa gwamnatin Buhari ba za ta iya magance talauci ba a ragowar watanni shida da suka rage mata.
Abu ne sananne da za a fahimta shi ne, yawa mara amfani wato talakawa sun yi kuskure wajen zaben mutanen da ba su dace ba. Haka kuma mutane ba za su ci gaba da maimaita kurakuran da suka yi a baya ba.
Hasashen zaben shugabanni ana yi ne bisa hujja da aka samu a kansu. Duk ‘yan takarar da suke neman wani mukami, dole su kawo manufofinsu wanda zai amfanar da talakawa.