Sarkin Hausawan Afirka Sardaunan Agadas, Dokta Abdukadir Labaran Koguna da hadin gwiwar majalisar al’ummar hausawan Duniya sun nada shugaban kwalejin kimiyyar koyon aikin lafiya na jihar Kano Dakta Bashir Bala Getso a matsayin Jakadan Hausawan Duniya kuma sarkin tsaftar hausawan Afirka.
Nadin an yishi ne a fadar Sarkin Dutse karkashin jagorancin mai martaba sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi cikin makon jiya wanda ya zo daidai da ranar Hausa ta Duniya.
- ‘Muna Kira A Samar Da Jami’an Tsaro Na Yankin Arewacin Nijeriya’
- “Akwai Matsala Game Da Bakin Da Ke Kwararowa Jihar Kano”
Nadin ya sami halartar dinbin jama’a daga sassa daban daban na kasarnan.
Nadin da aka yi wa Bashir Bala Getson na jakadan hausawan Duniya da kuma sarautar sarkin tsaftar Afirka na da alaka da gamsuwa da dinbin gudummuwa da yake bayarwa wajen bunkasa cigaban harkar lafiya a kasarnan.
Dakta Bashir Bala Getso ya nuna matukar farin cikinsa da wannan karramawa da akayi masa da hakan zai dada masa kwarin gwiwa wajen ayyuka da yake a fannin inganta lafiyar al’umma wanda sai da kyakkyawan yanayi na tsafatar muhalli ne lafiya ke inganta yanda yakamata.
Shugaban Kwalejin kimiyyar koyon aikin lafiya Jakada Sarkin tsaftar Afirka.
Dokta Bashir Bala Getso ya godewa masarautar hausawan Duniya da kuma Sarkin Hausawan Afirka kan dadinda akayi masa tareda godiya ga Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi wanda bisa sahalewar sane akayi masa nadin a masarautar Dutse ya kuma godewa wadanda suka zo daga sassa daban-dan shaida nadin da kuma taya shi murna.