Fursunonin shida daga gidan yarin Suleja sun sake samun ’yancinsu bayan wasu dalibai shida na makarantar Jewel Leading Light Academy da ke Abuja suka biya tararsu.
Daliban shida – Dave Falade, Otse Unogwu, Ife Atilola, Zachary Abu, Ugomsinachi Okoronkwo da Nathan Oyinlola – duk ‘yan aji 2 na babbar sakandare, sun yanke shawarar taimakon agaji.
- Ganduje Ya Yi Allah-wadai Da Dakatar Da Albashin Ma’aikatan Da Gwamnatinsa Ta Dauka
- Sarkin Musulmi Ga Shugabanni: Ku Guje Wa Rayuwar Almubazzaranci Domin Nijeriya Ta Ci Gaba
Daliban sun kai ziyara gidan yarin ne a ranar Talata, inda suka biya kudi Naira 120,000 a matsayin beli domin sakin fursunonin shida.
Haka kuma sun kai kayayyaki masu yawa ga wasu fursunonin da ke cibiyar.
Dangane da zaben fursunonin kuwa, daliban sun ce: “Mun ba da agajin tsabar kudi har Naira 120,000, tare da biyan tarar wasu fursunonin da suka nuna halin kirki da kuma sadaukarwa.”
Daliban da ke tsakanin ’yan shekara 11 zuwa 12, sun ce: “Mun tsayar da shawarar cewa a wannan aikin, za mu mai da hankali ne mu tara kudi da kayan aiki don tallafa wa ’yan’uwanmu da ke kurkuku.
“Yawancin lokuta, al’umma kan manta da kuma yin watsi da fursunoni. A matsayinmu na kungiya mun yanke shawarar cewa za mu sanya murmushi a fuskokin wadanda aka manta a cikin al’ummarmu.”
A cewarsu, sun tara kudin ne ta hanyar siyar da wasu kayayyaki a makaranta tare da neman tallafin ’yan uwa da abokan arziki domin tallafa musu.