Kungiyar daliban kwalejojin ilimi ta kasa ta yi kira da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan Nijeriya masu sha’awar bunkasa lamarin ilimi su kara taimakawa da kudi a matsayin bashi ko kuma taimako, domin taimakawa matasan Nijeriya da dalibai wadanda a halin da ake ciki basu da aikin yi, da idan ba sa a aka yi ba suna iya shiga wani hali na aikata ashsha,saboda halin da ake ciki na tsadar kayar abinci a sanadiyar karin kudin manfetur.
Sanarwar da Shugabanta Egunjobi Samuel Oluwaseun,ya raba wa manewa labarai ranar Litinin ta makon da muke ciki a Abuja, ya ce akwai dalibai milyan 12.5,a kwalejojin ilimi million 219 da ake da su a duk fadin Nijeriya,ya jinjina wa kokarin da Shugaban kasa yake yi kan rage fatara, inda kuma suka yi kira da shi cewar ya ci gaba da aiki mai kyau da yake yi.
- Ba Za Mu Shiga Zanga-zangar Da Za A Yi Wa Tinubu Ba – Daliban Arewa
- An Kashe Dalibai 3, An Raunata Wani A Harin Da Boko Haram Ta Kai Makarantar ‘Yan Shi’a A Yobe
Ya ce, “Idan aka kara kudaden yin hakan zai zai kara taimakawa a kan irin tubalin yin ginin hakan da aka fara wadanda gwamnatocin baya suka yi, wanda kuma hukumar NIRSAL ce jagorar yin hakan ta hanyar Microfinance Bank (NMFB), wanda ya samar da ayyukan yi a kai tsaye ko kuma akasin haka, lamarin da yayi sanadiyar raba wasu da fatara.”
Kunguyar ta dalibai ta jinjinawa jagorancin Abdullahi Abubakar Kure a matsayin Shugaban na Bankin Microfinance karkashin NIRSAL,kan irin namijin aikin da yake yi.
Ya kara jaddada cewa NMFB ita kadai ce hukuma wadda ta raba kudaden kawo dauki a cikin gaskiya da rikon amana,a sassa shida na kasa.
“Mutane sun samu dama ta samun bashin ba tare da taimakon wani daga cikin ofishin ba, maganar gaskiya kuma ire-iren wadancan kudaden ta ba wasu damar ga matasa bunkasa sana’arsu, wasu kuma sun fara, da kuma cigaba da harkar har zuwa halin da ake ciki yanzu” kamar yadda yace.
“Duk da yake dai wadanda suka amfana da kudaden sun so ace anbasu kudaden a matsayin tallafi ne amma Bankin ya cigaba da fada masu ai bashi ne aka basu.Duk dai yadda abin ya kasance kudaden sun taimaka wajen bunkasa kananan sana’oi a Nijeriya.
Daga karshe ya ce “Idan aka tuna da tsarin mulkin gwamnatin Shugaban kasa Bola Bola Ahmed Tinubu, abu maikyau ne da kuma fa’ida ga ita gwamnatin ta shi ta kara bada kudade a bangarori na kanana da matsakaitan sana’oi da kuma aikin gona, domin hakan zai taimakawa ‘yan Nijeriya su samu hanyar da za su dogara da ita saboda su samu kyakkyawar rayuwa,”.